Friday, 20 April 2018
Ka janye maganarka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari

Home Ka janye maganarka sannan ka ba matasan Najeriya hakuri – Shehu Sani ya shawarci Buhari
Ku Tura A Social Media

Sanata Shehu Sani yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba matasan Najeriya hakuri kan furucin da aka ce yayi na cewa matasan Najeriya yan cima-zaune ne. Sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a 20 ga watan Afrilu inda ya bukaci shugaba Buhari da ya janye kalaman nasa. Ya kara da cewa shugaban kasar ya fadawa matasa abunda yayi masu da kuma wanda zaiyi masu a nan gaba. 

A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari na ci gaba da shan caccaka bayan jawabin da yayi a kan matasan Najeriya a kasar Ingila. Kalaman ya fusata matasa da dama sannan kuma ya ba masu adawa da shugaban kasar damar tofa albarkacin bakinsu inda suke ci gaba da tunzura matasa. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: