Wednesday, 25 April 2018
Jami'an Hisba Sun Tsare Wata Bishiyar Da Ake Bautawa A Kano Karanta cikin Hotuna

Home Jami'an Hisba Sun Tsare Wata Bishiyar Da Ake Bautawa A Kano Karanta cikin Hotuna
Ku Tura A Social Media


Wannan abin al'ajabi ya faru ne a wani kauye mai suna Dorawar Tazalli dake karamar hukumar Kunci dake jihar Kano. Inda aka sami wasu gungun mutane sun tare a wata bishiya suna zuba ruwa a jikinta suna sha da nufin warkewa daga cutuka. Wasu kuma suna zagaya ta da niyyar yin dawafi.

Tunda fari dai wasu ne suka yi kururuwar cewar ana samun tabaraki a jikin bishiyar, wanda hakan ya sa hukumar Hisba ta shiga bincike domin gano gaskiyar lamarin. Amma daga bisani ta gano akwai alamun damfara.

 Hakan ya sa hukumar ta tashi jami'anta suka je domin sare bishiyar.

Saidai an yi gumurzu da wadanda ake zargi da zane a jikin bishiyar har ma an ji wa wasu jami'an Hisbar munanan raunuka.

Hakan ne ya sa wakilinmu ya je har Ofishin kwamandan, wato Malam Aminu Daurawa domin jin matsayin hukumar akan wannan lamari. Kuma ya yi bayanin matsayin su tare da cewar wannan wata sabuwar damfara ce. Kuma ya bayyana cewar tuni sun sare wannan bishiyar saboda gudun kada ta koma wajan bauta.

Haka kuma Malamin ya ce zanen da aka gani na dakin Allah kuma ake yin dawafi, wannan tantagatyar karya ce.

Daga karshe ya yi kira ga Malamai da su dinga shiga kauyuka domin fadakar da jama'a.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: