Monday, 23 April 2018
Akwai Yiyuwar Komawar Jaruma Sadiya Gyale Shirin Fim

Home Akwai Yiyuwar Komawar Jaruma Sadiya Gyale Shirin Fim
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar tsohuwar jarumar nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood wadda aka fi sani da Sa'adiyya Gyale ta yi karin haske game da yiwuwar dawowar ta shirin harkar fim musamman ma idan tayi na'am da irin rawar da za ta fito.

Mun samu dai cewa jarumar tayi wannan karin hasken ne a yayin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu lokacin da aka tambaye ta ko za ta iya fitowa fim a halin yanzu inda ita kuma ta bayar da ansa da cewa ya danganta da irin fim din da kuma rawar da za ta taka.


Haka ma dai da aka tambayi tsohuwar jarumar ko wace shawara za ta ba sauran mata masu harkar fim sai ta ce ta na yi masu fatan alheri, kuma tana ba su shawara da su rike sana’ar fim da kyau domin samun cin moriyar ta.

Labarin dae ke  cewa a watannin baya ne mijin jarumar ya rasu bayan sun shafe shekaru da dama a tare tare kuma da tara zuri'a ta 'ya'ya.

Haka zalika dai tun kafin nan a shekaru da dama da suka gabata jarumar ta yi aure a lokacin da tauraruwar ta take cikin ganiyar haskawa a duniyar shiya fina-finai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: