Yau Take Sallah : Ana Tuhumar Luca Modric Da Yiwa Kotu Karya

Hukumomi a Croatia na tuhumar kaftin din kasar Luca Modric da shan rantsuwar karya a kotu.
Ana zargin dan wasan na Real Madrid da yi wa kotu karya a lokacin da ake shari'ar Zdravko Mamic babban daraktan Dinamo Zagreb kan badakalar haraji.
Masu gabatar da kara sun ce Modric ya bada shedar karya a watan Yunin 2017 kan bayanan da suka shafi musayarsa daga Dinamo zuwa Tottenham Hotspur a 2008.
Idan dai har aka tabbatar da zargin, Dan wasan na iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.
An ce Mista Mamic da dan uwansa Zoran sun taushe wasu kudade ne a cinikin 'yan wasan Zagreb.
Ana zarginsu da wawushe kudaden Dinomo Zagreb da suka kai sama da $16.7m.

Share this


0 comments:

Post a Comment