Friday, 23 March 2018
Tsabar Rashin Adalci da Munafurci Ne Suka Hana Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Yin Magana Akan Abinda Fatima Ganduje tayi~Maryam Booth

Home Tsabar Rashin Adalci da Munafurci Ne Suka Hana Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Yin Magana Akan Abinda Fatima Ganduje tayi~Maryam Booth
Ku Tura A Social Media

Da take mayar da martani akan maganar da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yayi na cewa hukumar Hisba bata da hurumin kama diyar gwamna akan shagalin da akayi a bikinta, 
tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta bayyana cewa, tsabar rashin adalci da munafurci ne suka sa malamin ya fadi haka.

Ta kara da cewa idan da ace 'yan  fim ne suka yi wancan abu da an jishi da hujjoji kala-kala yana Allah wadai da su 
Amma gashi yanzu diyar gwamna tayi yana tambayarsu wai ya suke so yayi.

Maryam ta kara da cewa idan be yi kame ba wannan ba matsala bace 
amma irin yadda ya shafe kusan watanni yana sukar masu neman na kansu don rufawa kansu da iyalansu asiri wato 'yan Fim 
ya kamata ace ya fito koda rana daya ne ko kuma ma awa daya yayi magana akan wannan lamari, 

Maryam Booth ta kara da cewa su malaman da suka soki abinda diyar gwamnan tayi me ya faru dasu?,

Wato baza ka iya taba masu kudi ko mulki ba sai talakawa ko, don kada a sauke ka daga kujerar ka, 
to ka sani komin daren dadewa ba zaka dawwama akan wannan kujera ba, bayan mulkinsu watarana sai ka sauka.

Maryam ta kara da cewa kana hada siyasa da addini, baka so ka batawa uban gidanka rai, to saika shirya abinda zaka gayawa Allah a ranar tashin kiyama, ka bar aikinka na dora mutane akan hanyar shiriya saboda siyasa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: