Kannywood

Sharhin Fina Finai : Sharhin Fim Din Matan Aure

Daga Saddika Habib Abba 09097438402
[email protected]

Suna: Matan aure

Tsara labari: Abdullahi Amdaz

Furodusa: Umar M Sharif

Bada umarni: Abu Sarki

Kamfani: A Skuare Century, a dibision of Abu Sarki Inbestment Nigeria Limited
Jarumai: Ali Nuhu, Fati Washa, Halima Atete, Amina Amal, Fati S.U, Nafisa Abdullahi da Rabi’u Rikadawa

Sharhi: Saddika Habib Abba

A farkon fim din an nuna Alhaji Garba Dan Bahaushe (Ali Nuhu) tare da matarsa Hajara (Fati Washa) ta rako shi zai yi tafiya yana tabbatar mata da alkawarin bazai kara aure ba ita kadaice matarsa kuma an nuna ita bahaushiya ce suna zaune a garin Kano ne, bayan ya saka kafa ya tafi bai zarce ko ina ba sai garin Niger anan kuma an nuna yana da saka ranar wata yarinyar akansa Surayya (Fati SU) wadda ita kuma banufiya ce ‘yar asalin Niger din ce, a wannan garin har ya tsaya aka daura masa aure da ita ba tare da ta san yana da aure a Kano ba, bayan sun gama cin amarci shi da ita ya tsallaka ya tafi garin Maiduguri wanda yake da kamfani a garin, anan ma ya hadu da Falmata (Halima Atete) ya aureta kuma itama bai fadamata yana da aure ba daga nan itama bayan an gama cin amarci ya tsallaka jihar Adamawa ya hadu da Rahma (Amina Amal) ya aure ta kuma itama ya yi mata alkawarin ita kadaice bazai kara aure ba, acikin matansa hudu kowacce idan ta yi masa waya tana bukatarsa sai ya yi mata karyar aiki ne ya yi masa yawa ana cikin haka kwatsam Alhaji Garba sun taho da direbansa da manajan kamfaninsa a hanya za suyi tafiya sai suka yi hatsari da Alhaji Garba da direba suka mutu shi kuma manaja ya kwanta a asibiti rai a hannun Allah, bayan labarin mutuwarsa ya sami iyalansa kowacce ta baro garinta ta taho Kano karbar gado domin dukkaninsu mutuwarsa bata dame su ba gadonsu kawai suke ji, bayan sun zo gidansa na Kano domin dama kafin ya rasu ya fadamusu kwatancen gidansa amma sai ya yi musu karyar gidan iyayensa ne amma da suka zo sai suka tarar ashe matarsa ce wato Hajara wadda itama tare da mahaifinta Sunusi (Rabi’u Rikadawa) suna ta kasafin gadon da zasu samu katsam kuma sai ga ragowar matan sun zo anan fa fada ya kauraye kowacce tace ita kadaice matarsa duk ragowar macuta ne sun zo ne domin suci gado, mahaifin Hajara ba tare da bata lokaci ba ya maka kara kotu domin yace ‘yarsa ita kadaice matar Alhaji Garba Dan Bahaushe, bayan sun je kotu Alkali ya yi umarni akan kowaccensu ta kawo sheda wadda za’a gamsu da ita suka je suka kawo masa inbitation na daurin aure yace musu bai yarda ba domin na’ura mai kwakwalwa zata iya yi, su sake kawo wata shedar kowaccensu ta ce manajansa Ahmad shine shaidarta domin da shi duk aka je neman aurensu Alkali ya yi umarni aje idan da yuyuwa a taho da Manaja likitansa ya hana a taho da shi sai da akayi dauki ba dadi da likitan da Sunusi sannan ya bada shi ranar da za su koma kotu ya bada shaida sun dakkoshi sun taho hanya manaja ya rasu, hankalinsu ya tashi domin ya rage basu da wata sauran sheda kenan, suka fadawa Alkali halinda ake ciki ya yi umarni da kowccensu taje garinsu ta taho da waliyyinta wanda ya daura mata aure sannan a taho da wanda Alhaji Garban ya tura suka karbo masa auren kowacensu, sannan Alkali ya dage karar, bayan sun dawo katu kowaccensu ta hallara tare da mahaifinta da kuma abokan Alhaji Garban wanda ya tura suka nema masa aurensu, kowannensu ya gabatarwa da Alkali kansa da kuma matsayinsa a shari’ar bayan sun gama Alkali ya umarci kowannensu ya rantse da Alkur’ani mai girma ba tare da bacin lokaci ba kowannensu ya rantse Alkali ya amince sannan ya yanke hukuncin zai raba musu gado ana cikin haka sai ga wata matar Talatu ta shigo cikin kotu da ‘ya’ya guda biyu tace itama matarsa ce tun a kauye ita ya fara aura, talauci ne ya saka ya baro kauyen ya barta ita da mahaifiyarsa bai sake komawa ba sai yanzu ta ji labarin ya rasu, shine tazo domin ta sanar da halin da take ciki, Alkali ya umarci itama Talatu da ta yi rantsuwa a take a gurin ta rantse Alkali ya gamsu sannan ya ba da tabbacin cewar za’a bata abinda ta kashewa ‘ya’yansa da ita kanta tun daga lokacin da ya saka kafa ya fita har ranar sannan kuma ragowar dukiyar idan an raba za’a bata hakkin ‘ya’yanta domin tunda har ya auri mata hudu bayanta ita ba matarsa bace kamar yanda addini ya hukunta, Talatu ta gamsu da hakan amma su ragowar matan ba a son ransu ba babu wacce ta gamsu da hukuncin da Alkali ya yanke.

Abubuwan Birgewa:

1- Labarin ya sami tsari mai kyau sannan daraktan ya yi kokari gurin fassara labarin daga rubutu zuwa hoto mai motsi.
2- Jaruman sun yi kokari gurin isar da sakon yanda ya kamata.
3- An yi amfani da kayan aiki masu kyau kamar camera ta daukar hoto da kuma abin daukar sauti.

4- An fadakar akan wasu mas’aloli wanda ya shafi addini wanda sun fadakar sosai.

Kurakurai

1- An nuna Alhaji Garba a rayuwarsa ta kauye mutun ne mai kirki mai kuma tausayawa iyali amma sai gashi an ga ya barsu ya taho birni ya yi kudi kuma bai kuma waiwayensu ba har ya mutu duk kuwa da bayan iyalinsa ma harda mahaifiyarsa, yakamata ace tun a kauye an nuna shi mutum ne mara kirki don mai wannan halin irin nasa bazai aikata haka ba.

2- Alhaji Garba Dan Bahaushe ya taho birni a talauce kuma shi ba’a nuna ya yi karatu ba amma sai mai kallo ya ga ya kudance har ya mallaki kamfanunuwa shin ta wacce hanya ya yi kudi? yakamata a bayyanawa mai kallo.

3- Akwai gurinda aka nuna Alhaji Garba suna hira da Hajara yana yin karin kumallo kuma yana yabawa girkinta a lokacin cikin santi yakamata ace abinci aka gani a gabansa yana ci amma ba shayi ba tunda yana cewa girki girki amma sai mai kallo yaga ruwan shayi ne kawai sai kayan hadashi.

4- Akwai gurinda Alhaji Garba ya fantsamowa Falmata ruwan kwata yana cikin mota ba tare ya sani ba tana tsaye akan titi daga baya maikallo sai yaga ta biyoshi office dinsa tana yi masa korafi shin dama tasan shi ne da har tasan office dinsa? ko kuma tambaya tayi wani ya kwatanta mata?

5- Shigar da Rahma ta yi ranar da za’a kai ta gidan mijinta a lokacin da mahaifinta yake yi mata fada ba shiga ce irinta amarya wadda za’a kai ta gidan miji a ranar ba.

6- An ga Rahma a gurin gyaran gashi bayan an ganta mahaifinta yana yi mata fada kuma yace za’a kai ta a ranar, masu kallo sun san amarya tana yin gyaran gashi ne kafin ranar da za’a kaita yakamata ace wannan gurin gyaran gashin an fara yin sa kafin gurin da mahaifinta yace za’a kai ta a ranar.

7- Duk acikin surukan Alhaji Garba Dan Bahaushe ace an rasa wanda ya yi bincike kafin ya bashi auren ‘yarsa? idan kudi ne ya hana binciken kuma ai an nuna akwai mutanan kirki acikin surukan wanda su kudin baya gabansu kamar Sambo mahaifin Rahma duk mai ya hana su bincikawa?

8- Ta yaya za’ayi ace kana auren mutum ace bakasan kowa na sa ba kuma ka sami sukunin zama da shi da kai da iyayenka? hakan a gaske abu ne mai matukar wuyar faruwa.

9- Acikin tsarin harkokin kotun babu tsari aciki domin an ta fi da wasu abubuwan wanda bisa ka’ida ba.

Karkarewa:

Fim din ya kayatar da masu kallo, amma babu sako mai nauyi a ciki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button


WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?