Saturday, 17 March 2018
Sarkin Zamfaran Zurmi Ya Jagoranci Rabon Tallafin Shinkafa Buhu 1200 Da Sanata Kwankwaso Ya Baiwa Iyalan Wadanda 'Yan Bindiga Suka Kashe A kauyen Birane Dake Jihar Zamfara.(kalli hotuna)

Home Sarkin Zamfaran Zurmi Ya Jagoranci Rabon Tallafin Shinkafa Buhu 1200 Da Sanata Kwankwaso Ya Baiwa Iyalan Wadanda 'Yan Bindiga Suka Kashe A kauyen Birane Dake Jihar Zamfara.(kalli hotuna)
Ku Tura A Social Media

Daga Muawiya Abubakar Zurmi

A fadar mai mairtaba Sarkin Zamfaran Zurmi Alhaji Abubakar Atiku Muhammad yau Alhamis ma an cigaba da bada tallafin ga iyalai da 'yan uwan wadanda 'yan bindiga suka kashe a kauyen Birane, dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Tallafin da aka raba yau ya fito ne daga tsohon Gwamnan Kano Sanata Kwankwaso inda ya bada Buhu 1200 (25kg) na shinkafa, sai Kwamishina mai kula da 'yan gudun Hijira ta Nijeriya Hon Sa'adiya Umar Faruk inda ta bayar da tsabar kudi naira Miliyan daya hadi da tallafin, gero, masara, wake, gishiri da suka kai kimamin buhu 268. Sai kuma sabulun wanka, magunguna, injinan ban ruwa da dai sauran kayayyaki.

Rabon ya kasance kamar haka.

Duk wanda yake cikin wa'anda suka rasa rayukansu 'yan uwansa ko magadansa zasu karbi buhu ashirin da biyu 22 (25kg) na shinkafa buhun masara daya (1) Buhun Wake daya (1) Buhun gero daya (1) sai kudi naira dubu goma, dasauran kayayyaki.

Wa'anda suka ji rauni a wannan iftila'a kowane mutun daya zai anfana da buhun Shinkafa 7 (25kg) buhun masara daya buhun gero daya sai rabin buhun wake sai kudi naira dubu 10 da sauran kayayyaki.

Haka kuma a wajen wannan rabon tallafin an tuno da magada da yan uwan wa'anda suka rasa rayukansu a sanadiyar hare haren yan bindiga a shekarun baya a karamar hukumar mulki ta Zurmi wa'anda yawansu yakai mutun 46 suma anba yan uwan su tallafin buhuhuwan shinkafa 7 (25kg) da sauran kayayyaki.

Ga hotunan kayayaki da kuma yadda abun ya kasance:
Share this


Author: verified_user

0 Comments: