Thursday, 29 March 2018
Samun ƙungiyyar Matan Masana'antar Kannywood Abu Mai Matukar Amfani - Inji Saratu Gidado

Home Samun ƙungiyyar Matan Masana'antar Kannywood Abu Mai Matukar Amfani - Inji Saratu Gidado
Ku Tura A Social Media
Sartu Gidado Daso ta bayyana qungiyoyin da mata yan film
ke samarwa a yanzu domin taimaka wa ’yan fim da sauran
jama'a a matsayin wani mataki na ci-gaba da harkar ta
samu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin fitacciyar jaruma Hajiya
Saratu Gidado a lokacin da ta ke tattaunawa da wakilin
mujallar Fim dangane da irin yanayin da aka samu a cikin
masana’antar na bullowar wasu kungiyoyin mata da ke
taimaka wa jama’a marasa karfi.

Saratu (Daso), wadda a yanzu ita ce Jakadiyar Sarkin Kano,
ta ce, 

Wadannan kungiyoyi na taimaka wa marayu da
marasa karfi, musamman yara kanana da wasu da aka mutu
aka bar su. Wasu na yawon bara, wasu na yawon talla.

“To gaskiya kafa kungiyar ya burge ni. Na ji dadin yadda su
ka zauna su ka yi tunani su ka samar da wadannan
kungiyoyin.

Ka san babu mai iya wa mutum sai Allah. To amma dai ko
yaya ka samu ka taimaka wa na kasa da kai ka na da lada
mai yawa. Kuma kai ma da ka ke da hali ba ka san yadda
za ka kasance a gaba ba, amma dai alheri ba ya faduwa
kasa banza.”

Ta ci gaba da cewa, “Yanzu wannan aikin alheri da aka fara
mutane za su san cewa ’yan fim su na da tausayi, mu na
taimakon bayin Allah mu ma. Duk da ake yi mana kallon
wasu mutane na daban, mu ma mu na aimakon, don haka
yanzu mun fito mu na taimaka wa mutane kamar yadda ake
gani su na yi duk da dai ba na cikin kowace kungiya saboda
hidima ta ni ta yi min yawa don haka ni nawa taimakon ba
a bayyane na ke yin sa ba. Don haka ban shiga cikin
kungiyoyin ba, amma ina da labarin abubuwan da su ke yi,
kuma ina goyon bayan su dari bisa dari.”

A game da kasa kungiyoyin kashi-kashi, kowa ya na yin
tasa, Saratu ta ce, “To ai ba an rabu ba ne kuma ba ana
fada ba ne, kowa ya na da tsarin sa na yadda zai bayar da
nasa taimakon.
“Haka idan wata kungiya ta kai tallafi ga iyalan ’yan fim
da aka rasu aka bar su da kuma wadanda ba su da karfi,
wata kungiya kuma ta kai tallafi gidan marayu, wata kuma
ta kai tallafi asibiti, ka ga ai an samu ci-gaba. Kowa da irin
tallafin da ya ke ganin zai iya bayarwa ga jama’a. Don
haka samun karin kungiyoyi masu bada tallafi abu ne mai
kyau, kuma ci-gaba ne.”
Daga karshe Saratu ta yi kira ga al’umma da su bada
gudunmawar su, musamman ma ’yan fim, domin ganin
wadannan kungiyoyi sun samu nasarar da su ke bukata ta
taimaka wa mabukata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: