Saturday, 17 March 2018
Sabon Fim Din Bajrangi Bhaijaan Ya Samu Kudi Har Dala Miliyan 31.9 A Sati Biyu

Home Sabon Fim Din Bajrangi Bhaijaan Ya Samu Kudi Har Dala Miliyan 31.9 A Sati Biyu
Ku Tura A Social Media
Sabon fim din Salman Khan, na Bajrangi Bhaijaan, ya samu ribar kudi da ya wuce Rupee 200 a kasar sin, bayan da ya cika makonni biyu da sakar fim a gidajen kallo a Sin.

Masanin harkokin cinikaiya Tarhan Adarsh, ya sanar da haka a shafin sa na twitter, ya rubuta cewa Bajrangi Bhaijaan, ya yi nuni mai kyau a sati na biyu a kasar.
Fim din ya kuma tsallake makin rupee 200 a sati na 2, ya kuma rubuta tarin hikimar fim din a shafinsa na tweeter.

Daga ranar litinin zuwa yau Juma’a Fim din Bajrangi Bhaijaan, ya samu jimlar kudi dala miliyan 31.09 wanda yayi daidai da kudin India Rupee miliyan 201.71.
Wannan fim wanda Kabir Khan, ya kasance darakta yayi muhimmanci a kasar India, fim din ya nuna tauraruwa Kareena Kapoor, Khan da Nawazuddin Siddiqui, ya nuna labarin wata ‘yar shekara shida mai suna Munni wace Harshaali Malhotra da Bajrangi aka Salman, wanda yake bautawa Hanuman, ya dauki a niyar taimakawa yarinyar sake haduwa da iyayenta a tsallaken iyakar Pakistan bayan sun rabu.

Domin sauraren wannan labari sai ka latsa wannan link

Download Audio here 

Sources:voahausa.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: