Kannywood

Rayuwar Mace A Masana’antar Fim Abu Ne Mai Kyau

Da yawa wasu na ma matan da ake damawa da su a fagen fina-finai wani gani-gani, watakila saboda yadda suke kallon abin. Wadanda suke da irin wannan ra’ayin, Jaruma MARYAM SPARKLING ta warware musu yadda abin yake, inda ta bayyana irin alfanun da ‘ya mace take samu a rayuwar da take yi a masana’antar. To ko mene ne wannan? Wakiliyarmu JUMMAI IBRAHIM ta zakulo bayanin haka daga bakin Maryam wadda ta tattauna da ita a kwanan nan. Masu karatu; mu je zuwa:

Muna so mu ji cikaken tarihin rayuwar ki.

Masu karatu Assalamu alaikum. Da farko sunana Maryam. Kuma ni ’Yar jahar Kaduna ce. Amma usilin kauyenmu Kafanchan. Kuma ni ’yar Kudancin Zariya ce. Shi ya sa wasu abokaina sun fi sani na da Maryam Zariya ko kuma ‘sparkling’ Maryam. Shi ‘sparkling’, daga sunan salon da na fito. Na sa wa salon suna ‘sparkling’. Toh, sai abokan suke ce min ‘sparkling’ maryam.
An haife ni a Zariya. Kuma na girma a Zariya da jihar Katsina. Na yi furamare dina a L.E.A Ja’afar Zariya. Kuma na yi sakandare dina a ‘comprehensibe college’ Zariya. Daga nan sai na wuce Nuhu Bamali ‘polytechnic’. Inda na yi ND da HND, inda na nazarci aikin jarida. Kuma na yi PGD (Babbar Difiloma) a jami’ar jihar Kaduna 2014/2015.

Yaushe kika fara fim din Hausa kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga?

Da na gama karatuna a 2012 sai na shigo masana’ar tan fim. Farkon fim dina ‘Ranar Aurena’ a 2012 na kamfanin Mudansur Baruma ‘Mobies’.

Yaya kike kallon rayuwar mace a fim fagen yanzu?

A matsayina ta ’Ya mace a masana’ar fim zance kamar dama ce. Domin gaskiya harkar masana’antar fim kamar Makaranta ce. Kamin ka shiga za ka ga kamar abin wasa ne. Sai ka Shiga za ka gane aikin da gaske ne. Gaskiya rayuwa ’Yar mace a masana’antar fim abu ne mai kyau a gare ni. Domin a koda yaushe ina alfahari da abubuwa da nike koya daban- daban. Kamar kalmomin Hausa. Da sauransu. Da, na yi karatun Hausa a jami’a. Amma gaskiya karatun Hausa a yadda nike gani bai da iyaka. ‘So’, na ji dadin hakan gaskiya. Gaskiya, ban da abin da zance illa Alhamdu lilah. Domin Allah shi ne abin godiya.

A matsayin ki ta sabuwar jaruma wane irin tarba kika samu?

Akwai, kalubale kala-kala. Za ka ga wani yana yi da kai, wani kuma ba ya yi da kai. Ire-iren haka dai. Sai ka ga an kira ka aiki amma, sai wani ya sa a cire sunanka. Saboda ba ya son yi da kai. Toh, gaskiya ire-iren wanan, ya kamata a daina irin haka a masana’artar.
Ko Kina da sha’awan zama darakta ko mai fitar fim na kanki bayan kin yi aure?
Tabbas, ina da sha’awar hakan. Saboda sana’a ce, kuma mai kyau. Ban gan wata matsala a hakan ba.

Yaya batun aure, yaushe za mu sha biki, kuma waye angon, dan fim ne shi ma?

(Dariya sosai). Masha Allah, toh shi aure nufin Allah ne. Kuma ina rokon Allah ya zaba mani mafi alheri a gare ni. A duk lokacin da miji ya fito zan yi aure. Amma, kamin nan, ina da sha’awa a kan fim. Domin ina son na ga na ilmantar da jama’a da yawa ta hanyar fim, kuma ina son na ga jama’a suna alfahari da ‘Kannywood’ (murmushi).

Ko shin bayan fim kina wata sana’ar ta daban?

A gaskiya ni ’Yar jarida ce. Kuma, ina da dan shagona a Zariya inda ake yin salon da kuma sai da kayayyaki a ciki….kayaki irin na maza da mata.
Mun gode sosai da hadin kan da kika ba mu, Allah ya taimaka
Na gode da damar nan da kuka ba ni. Allah ya bar zumunci.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button