Thursday, 8 March 2018
Ranar Mata Na Duniya : Matan Arewa 5 Da suka kafa Tarihi a Nijeriya (hotuna)

Home Ranar Mata Na Duniya : Matan Arewa 5 Da suka kafa Tarihi a Nijeriya (hotuna)
Ku Tura A Social Media

Don taya iyayen mu mata raya wannan gangarumar ranar ga wasu matan arewa 5 da suka kafa tarihi bisa mukamin da suka samu sakamakon gwagwarmayar da suke
   
Tsohuwar ministan muhalli na Nijeriya Amina Muhammed
Hakika iyayen mu mata musaman yan arewa sun taka kuma suna cigaba da taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban bisa gudunmawar da suke badawa.
Ranar 8 ga watan maris na ko wace shekara majalisar dinkin duniya ta ware ta a matsayin ranar mata domin bikin nuna cigaban da mata suka kawo a duniya.

Bisa wannan dalilin muka kawo maku wasu matan arewacin Nijeriya fara kafa tarihi ta hanyar zamowa mata na farko da suka rike wani mukami. Ga su kamar haka:

1. . Amina Muhammed


Amina  Muhammed ce mace ta farko 'yar Najeriya da ta zama mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya. 'Yar asalin jihar Gombe ce kuma an haife ta a shekarar 1961. Ta samu wannan mukami a watan Fabrairun 2017.
2 Naja’atu Bala Mohammad

Naja’atu Bala Mohammad ce mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar daliban jami’a a Najeriya. An haife ta a garin Kano a shekarar 1966. Ta zama shugabar dalibai lokacin tana karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.3.Farfesa Fatima Batoul Mukhtar

Farfesa Fatima Batoul Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama shugabar jami’a a arewacin Najeriya. An haife ta a 1963, 'yar asalin jihar Kano ce. Ta zama shugabar Jami'ar Tarayya da Dutse a 2016.


4 Justice Maryam Aloma Mukhtar


Justice Maryam Aloma Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama babbar mai shari’a a Najeriya. An haife ta a 1944 kuma 'yar asalin jihar Kano ce. Ta samu wannan mukami a shekarar 2012.


5. Justice Zainab Bulkachuwa


Justice Zainab Bulkachuwa ce Mace ta farko da ta zama babbar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya. An haife ta a 1950 kuma 'yar asalin jihar Gombe ce. Ta samu wannan mukami a shekarar a 2014.

Banda su, ku bayyana sauran matan arewa da su suka taka rawar gani bisa gudunmawar da suke bada wa wajen raya al'ummar mu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: