Friday, 9 March 2018
Na Yi Nadamar Barin Barcelona - Neymar

Home Na Yi Nadamar Barin Barcelona - Neymar
Ku Tura A Social Media
Wani sabon labari da ya bulla a baya bayan nan ya bada tabbacin cewa dan wasa gaba na PSG mafi tsada a duniya, da ke jiyyar rauni Neymar, ya fara tuntubar jami’an tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona da nufin yi mata kome.

Wata jaridar labarin wasanni ta Spain, 'Mundo Deportivo', ta rawaito cewa tuni Neymar ya bayyana nadamar sauyin shekar da ya yi daga tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona zuwa PSG, kwanaki kadan bayan fitar da ita daga gasar zakarun turai da kungiyar Real Madrid ta yi da kwallaye 5-2 a jimillar wasanni 2 da suka buga.

Wannan sabon al’amari ya bijiro ne, watanni 7 kacal bayan sauyin shekar da Neymar ya yi daga PSG akan euro miliyan 222.

Sai dai fa ba wai Barcelona Neymar ya ke kallo kadai a matsayin hanyar samun damar raba gari da PSG ba, Real Madrid ma na daga ciki, kasancewar tuni shugabancin Madrid din ya ce a shirye yake ya biya euro miliyan 400 domin sayen dan wasan daga PSG.

Wasu masu sharhi na da ra’ayin Neymar yana neman hujjar komawa ne zuwa Real Madrid kai tsaye cikin sauki, kasancewar akwai yiwuwar Barcelona ta ki amincewa da tayin komensa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: