Monday, 5 March 2018
Munyi Fim Din Rariya Domin Iyaye Su Kula da Tarbiyya Da Halayar 'ya'yansu Da Suke Turawa Babba Makaranta Inji - Rahama Sadau

Home Munyi Fim Din Rariya Domin Iyaye Su Kula da Tarbiyya Da Halayar 'ya'yansu Da Suke Turawa Babba Makaranta Inji - Rahama Sadau
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa da na turanci (Kannywood & Nollywood) Rahama Sadau ta bayyana cewa babban makasudin su na yin film din rariya shine don su nusar da iyaye akan su lura da yaransu dake makarantun gaba da sakandire.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter a yayin da take maida martani ga wata ma’abociya shafin da tayi ikirarin cewa fim din rariya ka iya bisa abinda ta gani sanya ma iyaye rashin kwarin gwuiwar barin yaransu mata zuwa makarantun gaba da sakandire don fadada karatun su.

Sai dai jarumar wacce itace ta shirya wannan shiri ta maida martani da cewar fim din rariya anyi shi ne don ya haska ma iyaye akan su kasance masu sanya ido sosai a kan yadda yaransu ke rayuwa a makarantu don su gargade su akan su sani gami da kare mutuncin kansu, kar su biyewa mutanen da ka bige da yaudarar su da abin dunya don jefa su cikin wata rayuwa ta daban.

Film din Rariya na cikin fina-finan da akayi ikirarin sun kayatar sosai a fina-finan da suka fita a cikin shekarar data gabata, duba da yanayin yadda aka yi shi bisa wasu abubuwa dake faruwa a cikin al’umma.
Shin jama’a kun gamsu da wannan batu na jaruma rahama sadau?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: