Wednesday, 7 March 2018
Labari Da dumi-dumin: An Baiwa Maryam Sanda Beli

Home Labari Da dumi-dumin: An Baiwa Maryam Sanda Beli
Ku Tura A Social Media
Wata babban kotun birnin tarayya da ke zaune a Jabi Abuja ta baiwa Maryam Sanda , wacce ta hallaka mijinta, Bilyaminu Bello, beli.

Kotun ta bata beli ne akan dalilin cewa tanada juna biyu kuma ba tada lafiya. Alkalin kotun Jastis Yusuf Halilu ne ya bada wannan beli a yau Laraba, 7 ga watan Maris, 2018.

Lauyan Maryam Sanda, Joseph Daudu, ya bukaci kotun da ta taimaka ta ji tausayina bisa ga halin da take ciki domin ganin likitoci da kuma kula da cikinta.

Amma lauyan gwamnati, James Idachaba, ya nuna rashin amincewarsa da dalilin cewa tanada juna biyu kuma hujjan da ta bada na cewa tana juna biyu bai gamsar da su ba.

Maryam Sanda na gurfana a kotu bisa ga laifin kisan mijinta a cikin garin Abuja. Sau biyu kenan ta bukaci beli amma kotu bata amince be sai yanzu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: