Hotunan Matashin Mawaki Sa'eed Nagudu Da Amaryasa Da Zai Angwance

Mawaki Sa’eed Nagudu Zai Kara Aure
Fitaccen matashin mawaki kuma
Sa’eed Yahaya Abubakar wanda aka fi sani da ‘Sa’eed
Nagudu’ zai sake yin aure na biyu a cikin makon nan.

Za a daura auren mawakin da Amaryarsa A’isha Umar
Na’iyachi (Shatu) a ranar Asabar, 10 ga watan Maris
2018 a Masallacin Murtala da ke unguwar Hausawa a
cikin birnin Kano, da misalin karfe 11:00 na safe.

Amarya da Angon daman dai sun dade suna soyayya
tsakanin su wadda akalla sun fi shekara 7 a tare.

Inda su ka yi alkawarin aure a tsakanin su sai daga baya kuma
aka ga mawakin ya auri wata ‘yar uwar sa a shekarar da
ta gabata. inda har wasu suka rika tunanin ya yaudari
A’isha. Ashe komai da lokacin sa.

Za a gudanar da shagulgulan bikin ne kamar haka;
Friends day a Chicken Castle ranar 10th ga Maris
Walima ranar Juma’a a Batul Event Center, Gandu Bayan
Traid Fair, Za kuma a yi kamu a Gyadi-gyadi Court Road, a Bala
Mamsa Street Dan Amar Close.

In dai ba a manta ba Sa’ed Nagudu ya yi auren farko a
ranar 15 ga watan Satumba 2017. Inda ya auri wata ‘yar
uwar sa mai suna Khadija Ahmad Yusuf a garin su na
Jos.

Share this


0 comments:

Post a Comment