Friday, 23 March 2018
Gaskiya Abinda Ya Sanya Mutuwar Aure - Fati K K

Home Gaskiya Abinda Ya Sanya Mutuwar Aure - Fati K K
Ku Tura A Social Media
Kwanaki baya ana ta rade-radin auren fitacciyar jaruma Fati KK ya mutu, wai ma har ta kwaso kayanta daga Kano ta dawo Kaduna, kasantuwar ta ‘yar asalin garin na Kaduna ce, iyayenta duk su na Kaduna, aure ne kawai ya kai ta Kano.

Fati daman wannan auren na ta shi ne na biyu, ko da na ji an fara maganar ban yi wata-wata ba sai na neme ta a waya, ta kuma fayyace min komai ba ta boye min ba. Ban tsaya nan ba, na bi ta har gidansu na ce mata za ta iya magana a jarida game da mutuwar auren na ta? Ta ce da ni, eh, za ta iya, na zauna da ita ta koro min bayyanan ta kamar haka:

To ni dai abin da zan iya cewa, ni dai har ga Allah ya sani, wadanda muke tare da su su ma sun sani, na so zaman aure, na so zaman aure, na so zaman aure. In da ba na son zama da shi, wallahi ba zan mike kafafu na yi ta zuba ‘ya’ya ba.

Na fuskanci gori daban-daban duk na shanye, kuma hakan bai sa ni bijirewa ba har na ce a sake ni ba, na kan zauna in yi kuka, watarana sai na fada masa, sai na gane in har wani ya ki ka, ai Allah na son ka. Na fuskanci kalubale kala-kala, sai dai in ce mun gode Allah. Mun haihu da shi yara biyu, Abu ya ki ci, ya ki cinyewa, a gaskiya talauci bai taba sa na ce zan rabu da wanda nake tare da shi ba. Na dai samu surutai a cikin danginsa, wai don zai kara aure ne na bijire masa na ce ya sake ni, Alhalin wallahi tallahi, wallahi tallahi, wallahi tallahi ban san wannan zancen ba, ban ma taba jin sa ba. Ni na isa na ce ba na son a kawo min kishiya, bayan ni ma na sami wata? Ya kamata a duba wannan maganar kin fahimce ni.

Don shi yana ganin in ya bata ni a idon mutane, shi kuma za a ga farin sa. Don na taba aure na fito yanzun ma na fita gidansa, kuma duk wanda ya duba aure na na farko ya san na ci wuya, wadanda suka je suka gani da wadanda suka ji labari kowa ya Shaida, to wa zan zauna in ba labari har in ce ga matsala di na.

To ni dai yanzun ya sake ni, kuma har na ma gama idda na, batun aure kuma ban ce ba zan kara yi ba, amma gaskiya ba yanzu ba. Saboda ni yanzu mazan ma tsoron su nake ji wallahi, nan ka yi aure ka haihu, can ka yi ka haihu, to ina dadin sa. Ni yanzu addu’a ta, Allah Ya kawo wanda in ya aure ni zai rike ni har iya tsawon rayuwata, da ni da ‘ya’yana, tamkar shi ya haife su. Kuma ni ba zan taba zagin shi ko aiban ta shi ba, Saboda uban ‘ya’yana ne, ba zan yi abin da yake yi ba, na duk inda ya zauna sai ya yi ta zagi na, har kanwata ya samu ya ce mata in Allah ya yarda sai na wulakanta, abin da ya manta babu wanda aka halicce shi da arziki a Duniya. Karshe dai ina masa fatan alheri.

Sources :Leadershiphausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: