Saturday, 24 March 2018
Bambancin 'Ya'yan Masu Mulki Da 'Ya'yan Masu Zabe - Shaikh Pantami

Home Bambancin 'Ya'yan Masu Mulki Da 'Ya'yan Masu Zabe - Shaikh Pantami
Ku Tura A Social Media

Sheikh Isa Ali Pantami ya ce, duk duniya a Najeriya ne kadai mutum ya ke jagorantar abinda babu 'ya'yan sa a ciki. 'Ya'yan su ba za su sha ruwan da 'ya'yan masu zabe ke sha ba. Makarantar 'ya'yan su daban da ta 'ya'yan masu zabe. Kazalika asibitin 'ya'yan masu zabe da na 'ya'yan masu mulki daban. Kai hatta maganin 'ya'yan masu mulki daban yake da na 'ya'yan masu zabe.

 Sheikh ya kara da cewa, shin ta yaya shugaba zai san matsalar wajen da ya ke jagoranta bayan babu 'ya'yan sa a ciki? Me kuma ya sa zai gyara tunda ba 'ya'yan sa a ciki? 

Daga kan Kansila, Shugaban Karamar Hukuma, Dan Majalisar Jiha Da Na Tarayya, Sanata, Minista, Gwamna, Kwamishina, Mashawarta, Daraktoci, Manyan Sakatarori Zuwa Shugaban Kasa, Ko Akwai Wanda Dansa Ya Ke Zuwa Makarantar Gwamnati?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: