Monday, 12 March 2018
AUDIO Khudbar Juma'a Mai Taken kyakykyakwar Dabi'a - Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo

Home AUDIO Khudbar Juma'a Mai Taken kyakykyakwar Dabi'a - Dr. Muhammad Sani Umar R/Lemo
Ku Tura A Social Media
Khudbar Juma'a Mai taken Kyakykyakwar Dabi'a. 

Dr.  Muhammad Sani Umar R/Lemo daga Masallacin Juma'a na Dorayi Kano.

9/3/2018

⏩ Yaku yan uwa musulmi kyakykyakwar dabi'a na sanya ma mutum samun dajara a nan duniya da gobe lahira. 

⏩ Manzon Allah s.a.w yace shin wa keson gobe kiyama yana tare dani muna tare sai yace sai mai kyakykyakwan dabi'a. 


⏩ Mutum mai yawwan azumin nafila da nafilolin dare babu mai ta ko irin wannan darajarsa sai mai kyakykyakwar dabi'a.

⏩ Manzon Allah s.a.w yace : babu abu mai shigar da mutune aljannah kamar masu imani, da kyakykyakwan dabi'u. 


⏩  Kyakykyakwar dabi'a na sanya al'umma da samun cigaba da nasarori a harkokin duniya da lahira. 


⏩   Kyakykyakwar dabi'a manzon Allah (s.a.w) yace : babu mutum mai samun ma'auninsa ya cika a gobe kiyama irin mutum mai kyakykyakwar dabi'a.  ⏩ Kyakykyakwar dabi'a na sanya al'umma tarbiyya da girmama manya da kame kai, sai kaji ana cewa zamani ne har da shuwagabani wannan ba wani zamani alama ce ta rushe al'umma musamman kaga har da 'ya mace mai kunya babu abu mai kawo mata daraja irin kyakykyakwar dabi'i saboda anfi sanin 'ya mace da kunya. 

Wannan kadan ne daga cikin wannan Khuduba sai ka latsa wannan link domin sauraron darajoji ga mai kyakykyakwar dabi'a da wanda Allah baya so. 

Download kyakykyakwar Dabi'a Dr sani R/lemo

Share this


Author: verified_user

0 Comments: