Thursday, 8 March 2018
Allahu Akbar: An bude Sabbin Masallatai 423, An Rufe Coci 500 a Birnin Landan

Home Allahu Akbar: An bude Sabbin Masallatai 423, An Rufe Coci 500 a Birnin Landan
Ku Tura A Social Media
- Addinin musulunci na kara samun karbuwa a birnin Landan inda ake ta bude sabbin masallatai da kotunan shariah 
 A halin yanzu an bude sabbin masallatai 423 a unguwani daban-daban wande ke maye gurbin coci-coci da kuma kotunan shariah 100 

- Wata kididiga kuma ta nuna cewa al'umman musulmi ne za su mamaye birnin saboda galibin su matasa ne Wani babban alama da ke nuna cewa addinin musulunci na karbuwa a Birnin Landan shine yadda ake ta gina masallatai da kuma kotunan sharia'ar musulunci a wuraren da a baya makil suke da coci-coci. 

A cewar wani mai wa'azin addinin musulunci, Maulana Syed Raza Rizvi, 'Birnin Landan ta fi wasu kasashen musulmi rayuwa cikin tafarki irin na addinin Islama' kamar yadda Your News Wire ta ruwaito.

Bugu da kari, an gina sabbin masallatai 423 a Birnin na Landan a wasu unguwanin da a baya coci ne ke wuraren, a wasu lokutan ma akan mayar da coci ta zama masallaci kamar yadda cibiyar bincike na Gatestone ta ruwaito. 

Jaridar Daily Mail na kasar Ingila ta fitar da wasu hotunan coci da masallaci da ke kusa da juna a birnin Landan, a gefe daya akwai katafaren cocin San Giorgio mai cin mutane 1,230 amma mutane 12 kawai ke ciki, a gefe guda kuma ga wani karamin masallaci mai cin mutum 100 amma ga dumbin al'umma sun cika titi suna sallah. Hakazalika, wata kididiga ta National Secular Society tayi ya nuna cewa galibin mabiya addinin kirista a Birnin Landan dattawa ne masu shekaru sama da 65 su kuma musulmai galibin su matasa ne yan shekara 25. Hakan na nuna cewa a gaba addinin musulunci ne zai mamaye Birnin na Landan. Birnin na Landan kuma cike ya ke makil da kotunan sharia, a halin yanzu akwai kotunnan shari'ah guda 100, hakan ya yiwu ne sabosa dokar kasar da ta bawa al'umma daman sulhunta kansu bisa wata dokar da suka amince da ita.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: