Wednesday, 21 March 2018
Abun Da Ya Faru A Bikin Auren 'Yar Gidan Gwamnan Jihar Kano Tsokanar Allah Ne — Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun

Home Abun Da Ya Faru A Bikin Auren 'Yar Gidan Gwamnan Jihar Kano Tsokanar Allah Ne — Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun
Ku Tura A Social Media

Irin abun da ya faru a Bikin Auren 'Yar Gidan Gwamnan jihar Kano, a Kano, Tabbas tsokanar Allah ne.

Akalla ranar Daurin Auren nan jiragen da suka sauka a Kano, a halin da kasar take ciki na rashin kudi, bai kasa jirgin sama arba'in ba, kuma Gwamnoni ba su kasa guda ashirin da biyu ba a gurin.

Sannan yarinyar nan ta mike a gaban iyayenta, a gaban surukanta, a gaban sauran jama'ah, tana Rawa tana tsotsar bakin mijinta, Hasbunallahu Wa Ni'mal Wakeel! Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!! Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!!

Kuma haka mafi-yawancin wasu dai-daiku ke yi idan za su aurar da 'ya'yansu, aje a kama guri, ayi coptel party, azo ga bangaren amarya, ga bangaren iyayenta, ga bangaren ango, ga bangaren iyayensa, azo su taru guri guda, ace za a yanka Keck, a tashi a wasa yarinya a wasa yaro, a tashi ayi clapping, ayi musu tafi, bayan anyi duk wadannan abubuwa, sannan ace za su yanka Keck, bayan an yanka Keck din nan, yarinyar ta tsikaro ainihin yankin Keck din, sai ya buda baki kamar hankaka, sai ta saka masa a baki, sai ayi tafi, wai an Ci gaba.

Bayan haka, shi ma sai ya sake tsikarowa, ya sa mata a baki, nan ma ayi tafi.

Haka fa ake yi a kasar nan, to Tsokanar Allah Ake Yi, kuma babu yadda za a yi mu kadaitu daga fitinun da ke faruwa a cikin mu, sai mun gyara wannan. Inji Shehin Malamin.

Allah Ya ba mu ikon gyara wa. Ameen.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: