Friday, 16 February 2018
Wasanmu da PSG a Faransa ba mai sauki bane - Zidane

Home Wasanmu da PSG a Faransa ba mai sauki bane - Zidane
Ku Tura A Social Media
Mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ya ce ‘yan
wasansa zasu iya shan wahala sosai a zagaye na biyu na
wasan da zasu yi tattaki zuwa Faransa don karawa da
kungiyar PSG, a gasar zakarun turai mataki na kungiyoyi 16.

A zagayen farko na wasan dai Real Madrid ta lallasa PSG da
kwallaye 3-1, wadanda Critiano Ronaldo da Marcelo suka ci,
yayin da suka karbi bakuncin PSG din a filin wasa na Satiago
Bernabeu.

Zidane dai ya yi gargadin cewa dole Real Madrid ta jajirce a
wasa na biyu da zata yi tattaki zuwa Faransa, ba tare da
la’akari da nasarar farko da suka samu kan kungiyar ba.
Tun a farkon kakar wasa ta bana Real Madrid ke fuskantar
kalubalen koma baya kan nasarorin da ta saba samu a
wasanninta, musamman na gida Spain wato La Liga.

Kalaman na Zidane sun zo ne a dai dai lokacin da shi ma,
dan wasan gaba na kungiyar PSG, Neymar, ya jadadda cewa
kungiyar tasa, zata iya kai wa ga zagaye na gaba a gasar
zakarun turan, duk kuwa da rashin nasarar da suka yi a
hannun Real Madrid a Spain, ranar Laraba da ta gabata.

Ko da yake Neymar ya ce wasan zagaye na biyu da zasu
fafata a ranar 6 ga watan Maris mai wahala ne, yana da
kwarin gwiwar zasu iya samun nasara akan yaran Zidane.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: