Kannywood

Wani Jarumin Finafinan Hausa Na Neman Hallaka Ni, Cewar Mawaki Nura M. Inuwa …

ana zagin halitta ta bayan an watsi min guba, cewarsa

Ga abinda mawaki Nura M. Inuwa ya bayyana

“Ga duk wanda ya ga hoton nan zai yi mamaki 
domin tunda nake ban taba dora shi a kowacce kafar sadarwa ba, sai dai na yi karo da shi kuma idan na yi karo da shi wuce shi nake yi. Saboda ba na bukatar ganin sa domin ba na so ya dinga tuna min yadda nake a baya, duk da kalubalan da nake fuskanta daga jama a na goranta mini da suke akan halitta ta kuma ba ni da ikon yin magana dan gudun kada a ce na fiya raki da habaice-habaice”.

“Bana tuna matsalar da ta same ni sai an goranta mini sannan nake tuna ni ma ba haka Allah ya yi ni ba, kaddara ce ta same ni kamar yadda na san babu wanda ya fi karfinta, ina kokarin jure abubuwan da ake yi mini a bayan fage domin na san zan iya shanyewa, ana yi mini abubuwa daban daban da nufin tsoratarwa”.

Kamar yadda yanzu nake dauke da sakon daya daga cikin yaran wani jarumin kannywood cewa sai sun karasa aikin su a kaina, kuma wai shege ka fasa a cewarsa.

Ban san ko waye ba, amma na san da akwai sunan jarumin tunda an fara wasan zan dora duka sakonnin da aka yi mini da kuma lambar.

Sannan a karshen ya ce ya san na tsorata.

To NURA M INUWA ALLAH daya nake tsoro ba mutum ba”

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button