Kannywood

Taƙaitaccen Tarihin Jaruman Masana’antar Kannywood Hassana Da Hussaina

Hassana Yusuf da Hussaina Yusuf fuskokinsu ba boyayyu ba ne musamman ga wadanda suke kallon fina-finan Hausa na Kannywood ko shirin wasan kwaikwayo na Dadin Kowa da tashar Arewa 24 ke haska shi inda ka fi saninsu da Gimbiya da Sa’adatu. A tattaunawarsu da Aminiya sun ce halayyar da aka ba su a wasan Dadin Kowa ta yi kusa da halayyarsu ta gaske. Kuma sun ce da zarar sun samu miji tare to za a daina ganin fuskarsu a fina-finai gaba daya:

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarku a takaice?

Hassana da Hussaina: Mu ’yan asalin Maiduguri ne. Mun yi karatun firamare da sakandare, mun yi Diploma a can inda na karanta Halayyar dan Ada, (Sociology) a Jami’ar Maiduguri. Bayan mun gama sai muka taho nan Kano inda dama can muna zuwa wajen dangin mahaifiyarmu. Amma insha Allah za mu dora da digriri nan gaba don muna da niyyar komawa karatu a nan Kano ko a Maiduguri.

Aminiya: Yaya aka yi kuka fara fim?

Hassana da Hussaina: Tun muna sakandare muka nuna sha’awarmu ta shiga fim, sai aka ce mana to mu bari sai mun kamala karatunmu. Bayan mun kammala sai muka taso da batun sai iyayenmu suka amince. Kuma a gaskiya mun shiga fim ne don mun dauki harkar a matsayin wata hanya ta fadakarwa, sannan sana’a. Wannan ne ya ja hankalinmu.

Aminiya: Kasancewarku baki lokacin da kuka zo Kano wa ya shige muku gaba a harkar?

Hassana da Hussaina: Eh gaskiya mutanen da suka nuna mana harkar nan suna da yawa. Daga cikinsu akwai wani marubuci Nazir Adam Salihi shi ya hada mu da Darakta Falalu A. dorayi. To daga nan muka fara fim. A Lokacin ni kadai (Hassana) na fara fitowa tare da jarumi Adam A. zango a cikin fim din kudiri. Daga nan kuma muka ci gaba da fitowa a fina-finai daban-daban. Daga baya kuma sai tashar Arewa 24 ta nemi mu rika yi mata wasan kwaikwayo na Dadin Kowa wanda a yanzu ma an fi saninmu a can, domin duk wanda ya ganmu da sunan da muke fitowa a Dadin Kowa yake kiranmu. A takaice dai Dadin Kowa ya danne fina-finanmu na Kannywood.

Aminiya: Duk da cewa ku ’yan biyu ne, yaya aka yi dukanku kuke sha’awar fim?

Hassana: Eh to an sha yi mana wannan tambayar, amma gaskiya ba za mu ce ga dalili ba. Kawai dai kaddararmu ce iri daya. Akwai wani mawaki da ya taba ce mana me ya sa muke fitowo a fim gaba dayanmu? Me ya sa daya ba za ta yi waka ba, daya kuma ta yi harkar fim? Sai muka ce masa ai ba mu da muryar da za mu yi waka.
Hussaina: Amma ni gaskiya a yanzu ina so in yi waka. Idan zan samu wanda zai shige min gaba zan yi. Misali idan na samu wani mawaki wanda zai koya min harkar sosai zan yi.

Aminiya: Zuwa yanzu fina-finai nawa kuka yi?

Hassana/Hussaina: Gaskiya suna da yawa ba za su kirgu ba, tunda wasu sai ka gama aikinsu sai a sauya musu suna. Tun daga 2015 da muka fara fim zuwa yau akwai su da yawa wasu ma yanzu muna kan aikinsu.

Aminiya: Wane kalubale kuke fuskanta daga ’yan uwanku a Maiduguri musamman idan kun je ganin gida?

Hassana/Hussaina: Duk da cewa duk irin abin da mutum zai yi a rayuwa sai ya samu masu magana, amma alhamdulillah mu dai ba mu da wannan matsalar duk da cewa ba za a rasa ba. Kowa ya san muna da dangi a Kano an san kuma a hannunsu muke to ina ganin shi ya sa muka samu sauki.

Aminiya: Batun aure fa yaushe ake sa ran yi?

Hassana/Hussaina: Dariya….Ko yanzu Allah Ya kawo aure za mu yi insha Allah, saboda mu a shirye muke mu yi aure. Sai dai muna burin mu yi aure tare, hakan ne ma ya kawo jinkirin auren, domin da a ce daban-daban za mu yi da tuni mun yi. Muna jiran Allah Ya kawo mana maza nagari, mu je kuma mu yi bautar Allah. Mu kuma ajiye harkar fim gaba daya.

Aminiya: Duk da cewa akwai dan bambancin a kamanninku wane hali ne kuma yake bambanta ku?

Hassana da Hussaina: Eh kamar yadda kika sani dole za ki samu ’yan biyu daya na da hakuri, daya kuma na da fada. To muma haka muke. Hassana tana da hakuri. Hussaina kuma tana da dan zafi. Wannan ya yi kusan yin daidai da halayyar da aka ba mu a wasan Dadin Kowa, duk da cewa a wasan an dan kara yawan fadan da tsiwar na Hussaina.

Aminiya: Yaya mu’amalarku take da mutanen gari?

Hassana da Hussaina: Kasancewarmu muna fitowa a fina-finai a yanzu kowa ya san mu. Duk inda muka shiga sai ki ga mutane suna nuna mu. Ko yanzu da muka fito sai da yara suka biyo mu suna nuna mu ga Gimbiya da Sa’adatu. Duk da cewa wani lokacin akwai damuwa, amma ba ya bata mana rai. Mun dauki abin a matsayin daukaka ce daga Allah muna yabawa, domin babu zagi tsakanimu sai ambaton alheri. A mafi yawan lokuta mukan tsaya mu gaisa da mutane. Idan yara ne kuma mu daga musu hannu mu wuce.

Aminiya: Wane sako kuke da shi ga masoyanku?

Hassana da Hussai
na: Tsakaninmu da masoyanmu sai godiya. Muna kuma yi musu albishir su kara sa ido nan gaba za su kara samun abin da suke so daga gare mu. Fatanmu Allah Ya bar mu tare. Mun gode, mun gode.

Daga Jaridar Aminiya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button