Sunday, 4 February 2018
Ga Wata Sabuwa Ina So Infi Mahaifi Na Suna a Harkar Fim - Ahmad Ali Nuhu

Home Ga Wata Sabuwa Ina So Infi Mahaifi Na Suna a Harkar Fim - Ahmad Ali Nuhu
Ku Tura A Social Media


Dan fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa a masana'antar fim watau Ali Nuhu mai suna Ahmad ya bayyana cewa yana da burin duniya ta san shi fiye da mahaifin sa a harkar.

Ahmad Ali Nuhu din dai ya bayyana hakan ne a cikin wata fira da yayi da wata mujallar fim a watannin baya inda ya ce yana da burin ya fi mahaifin nasa suna da kuma daukaka a harkar ta shirya fina-finan Hausa.

Ahmad Ali Nuhu din da ya fara fitowa a talabijin tun yana dan shekara biyar a duniya ya bayyana haka zalika ya bayyana cewa yana iya taka duk rawar da aka saka shi yayi a cikin fim yanzu haka dai-dai gwargwado.

Daga karshe kuma yaron jarumin ya yi wa masoyan sa da ma dukkan masu sha'awar fina-finan Hausa fatan alheri da kuma godiya tare kuma da rokon su rika basu shawara a duk inda suka ga ba dai-dai ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: