Sunday, 18 February 2018
Duk Duniya Akwai Kasar Da Ta Fi Nijeriya Abun Mamaki Kuwa? Daga Hajiya Jamila (Yar Baba Mataimaki)

Home Duk Duniya Akwai Kasar Da Ta Fi Nijeriya Abun Mamaki Kuwa? Daga Hajiya Jamila (Yar Baba Mataimaki)
Ku Tura A Social Media

 1. A Nijeriya ne Wani Kifi Ya hadiye Jirgin ruwa yana dauke da man fetur ganga dubu.

2. A nijeriya ne beraye suka kori shugaban kasa daga ofis.

3. A nijeriya ne wata macijiya ta hadiye naira miliyan talatin da shida.

4. A nijeriya ne aka baiwa wani ajiyan  man fetur kafin a Je a dawo aka tarar akuya  ta shanye rabin man.

5. A nijeriya ne aka zo da 'budget' ga shugaban kasa ga mataimakinsa ga 'yan majalisa amma ake nemi budget din sama ko kasa aka rasa Shi.

NI TSORO NA DA NAKE YI KADA WATA RANA A CE MANA BERAYE SUN SACE CBN.

 GASKIYA NE NIJERIA AKWAI ABIN MAMAKI KWARAI.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: