Thursday, 8 February 2018
Da Kyau Ina Matukar Son Nayi Aure inji Jaruma Sadiya Kabala

Home Da Kyau Ina Matukar Son Nayi Aure inji Jaruma Sadiya Kabala
Ku Tura A Social Media
A sakamakon yadda ra'ayoyi na rayuwa suke banbanta, wata fitacciyar jarumar fim ta dandalin Kannywood, ta bayyana yadda take matuƙar muradin aure, a yayin da wusu jaruman suke cewa ina ba yanzu ba sai sun shirya zuwa gaba.

Ita dai wannan jarumar ta fina-finan hausa, Sadiya Kabala, ta bayyana irin yadda tale son taga tayi aure a rayuwa, inda har take rokon Mai duka da cewar, Allah ka aurar da mu.


Sai dai addu'ar wannan jaruma ba ta taƙaita akan ta kadai ba, inda tayi jimilla wajen rokon Allah, wanda hakan ya nuna ba ita kadai ce jarumar dake buƙatar aure a halin yanzu ba.

Duniya ta fahimci cewa, akwai da yawan jaruman kannywood dake buƙatar aure, sai dai lokaci bai basu ikon samun abokan zama na rayuwar su ba, duba da kasancewar yanayi na rayuwa da mata suke ƙara yin yawa tare da samari ke gudun sa a sakamakon rashin abin hannu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: