Sunday, 18 February 2018
Ba Zamu Yarda A Mai Da Nijeriya Kasar Izala Ba __Cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Home Ba Zamu Yarda A Mai Da Nijeriya Kasar Izala Ba __Cewar Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Ku Tura A Social Media

Jiya Juma’a 16/2/2018, babban shehin malamin darikar Tijjaniyyah a tarayyar Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga shugaban kasan Nijeriya da Antoni Janar na kasa da duk wanda abin ya shafa da ba zasu yarda a haramta masa wannan “freedom of religion” da tsarin mulki ya basu ba ta hanyar hana ‘yan tijjaniyyah yin wazifa da karatun salatul fatih da taron Maulidi a makarantun gwamnati ba.

Shehin malamin yana cewa:
 “A kawo mana dokar Nijeriya wadda ta hana wazifa a Nijeriya, wadda ta hana yin karatun Salatul Fatih a Nijeriya, a kawo mana mu ga numba ta nawa ce, ta wacce shekara ce. Kawai don muna da kunya, muna da mutumci muna yin shiru! Sai a mai da kasar kasar IZALA? Wallahi ba zamu yarda ba.” 
Malamin yayi ishara ga gwamnati da ta lura sosai ka da ‘yan a bata su bata ma ta gwamnati ta hanyar jefa ta cikin rikimar da ba zasu iya mata maganinta ba. Yana cewa;
 “ …Ga rigimar makiyaya da manoma, yanzu kuma ‘yan tijjaniyyah a hana masu ‘yancin addini a makarantu bayan an rubuta “freedom of religion”, LAKUM DINIKUM WA LIYAD DIN. Lallai muna jan kunnen wa’yanda abin ya shafa.”

Malamin ya cigaba da cewa:
 “ Wacce doka ce aka kawo sabuwa ban da “freedom of religion”? Mu bama son tashin hankali, bama goyon bayan tashin hankali amma in an kore mutum ya rasa yanda zai yi, to, dole zai dauki doka a hannunsa. Allah Ya kiyaye, Allah Ya kiyaye.”

Shehin malamin ya kara da yake cewa su basu yarda wannan gwamnatin IZALA ce ba :
 “ Su ‘yan izala suna cewa wannan gwamnatin gwamnatin IZALA ce, bamu yarda ba, gwamnatin Nijeriya ce. Amma ana so a tabbatar ma mutane wannan gwamnatin gwamnatin IZALA ce. Ta soma hana wazifa, ta soma hana salatul fatih, ba zamu yarda ba wallahi. Ko gwamnatin soja tayi mana haka ba zamu yarda ba. Ai ba gwamnati sai da mutane, kuma mutane Alhamdulillahi muna da mutane wanda duniya take kallo da mutumci da addini da ilimi. A cikinmu ne fa akwai Sheikh Sharif Ibrahim Sale wanda shi abin nunawa ne a cikin dukkan duniya gabaki daya bare Nijeriya. Bayan sanin Alkur’ani da sanin hadisi da sanin riwaya da sanin ilimin addini shi Sharifi ne a wajen baba, Sharifi ne ta wajen mamanshi…..”

Shehi ya gargadi gwamnati yana cewa:
 “..Lallai gwamnati da duba wannan, saboda hakurinmu ya kare. Cin mutumcin da ake ma mutanen mu a makarantu a hana su wazifa, a hana su karatun salatul fatih, alhali kuwa dukkan makarantun na gwamnati ne, ban a IZALA bane.”
 “ Abin da aka dauko na cewa wannan gwamnatin IZALA ce, ta hana wazifa, ta hana karatun salatul fatih a bincika daga ina wannan hukunci ya fito. Ba zamu yarda ba wallahi.”
A karshe shehim malamin yayi wa kasar Nijeriya addu’a

Share this


Author: verified_user

0 Comments: