Tuesday, 27 February 2018
Ba za a Mu yi Amfani da Fasahar Alkalanci Ba a Turai- Ceferin

Home Ba za a Mu yi Amfani da Fasahar Alkalanci Ba a Turai- Ceferin
Ku Tura A Social Media
Hukumar Kwallon Kafar nahiyar Turai ta ce, ba za ta yi amfani da fasahar bidiyon da ke taimaka wa alkalin wasa a kakar gasar zakarun Turai mai zuwa ba saboda tarin rudanin da ke tattare da fasahar kamar yadda shugaban hukumar, Aleksander Ceferin ya bayyana.

Ceferin ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da cikakkiyar masaniya kan yadda fasahar ke aiki saboda rudanin da ke cikinta.
Ceferin ya kara da cewa, lallai wannan fasahar tana da kyau amma kar a yi garajen fara amfani da ita.

Kalamansa na zuwa ne a yayin da da Kwamitin Kwallon Kafa na kasa da kasa ya gudanar da wani taro a ranar Asabar don yanke shawara game da amincewa da fasahar kafin aiki da ita a gasar cin kofin duniya a Rasha a bana.
An dai yi amfani da fasahar a wasu kasahe kamar Ingila a gasar firimiya da Carabao da kuma Jamus a gasar Bundesliga, sai kuma Italiya a gasar Serie A.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: