Tuesday, 27 February 2018
Ba Za Mu Canja Ranar Zaben Shugaban Kasa Ba — INEC

Home Ba Za Mu Canja Ranar Zaben Shugaban Kasa Ba — INEC
Ku Tura A Social MediaHukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta jaddada cewa ba za ta canja ranar zaben Shugaban kasa ba kamar yadda majalisar tarayya ta nema a garambawul da ta yi wa dokokin zabe.

A bisa jadawalin zaben 2019 da hukumar INEC ta fitar a ranar 9 ga watan Janairu, ta tsara gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar tarayya a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2019 sai na gwamnoni da majalisunsu wanda za a yi a ranar 2 ga watan Maris amma kuma a gyaran da majalisar tarayya ta yi wa dokokin zabe, ta mayar da zaben Shugaban kasa ya zama na karshe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: