Monday, 19 February 2018
Ashe ba Ronaldo da Messi ne kan Gaba Wajen Yawan Dukiya Da Kudi a Cikin ‘Yan kwallon Kafa Ba

Home Ashe ba Ronaldo da Messi ne kan Gaba Wajen Yawan Dukiya Da Kudi a Cikin ‘Yan kwallon Kafa Ba
Ku Tura A Social Media
Faiq Bolkiah mai shekaru 19 a Duniya ya sha gaban har irin su Ronaldo

- Gidan wannan matashin ‘Dan kwallon ke rike da sarautar kasar Burnei

Kwanan nan mu ka gano cewa ashe wani yaro ne dabam ba manyan gwaraza irin su Ronaldo ba ne kan gaba wajen yawan dukiya a cikin jerin ‘Yan wasan kwallon Duniya ba. Iyayen wannan yaro sun taba biyan Marigayi Micheal Jackson Dala Miliyam 12 domin yayi masu wasa.

Ba Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne kan gaba wajen yawan dukiya ba
Dan kwallon da ya fi kudi a Duniya shi ne Faiq Bolkiah wanda da dama ba su da labarin sa don kuwa bai yi suna ba. Bolkiah mai shekaru 19 ma dai ko bugawa Kungiyar sa ta Leicester City bai taba yi ba a halin yanzu don kuwa yana sahun masu tasowa ne a Kungiyar.


Kamar yadda jaridun kasar waje ke bada rahoto, ‘Dan wasan ya mallaki abin da ya haura Biliyoyin Daloli. ‘Yan uwan wannan saurayi ne ke da rike da sarautar kasar Burnei wanda sun ba Dala Biliyan 20 baya tuni. Dan wasan ya bugawa Chelsea kafin ya koma Leicester.

An haifi wannan ‘dan gidan sarauta ne a Garin Los Angeles Kasar Amurka amma yanzu haka yana bugawa kasar sa ta Brunei inda har ya taba cin kwallo guda. Mahaifin wannan matashi yana da motoci sama da 2300 kuma mutum ne mai facaka da kudi kamar ba ya so.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: