Saturday, 24 February 2018
Ana Rikici Tsakanin Mourinho Da Paul Pogba A Filin Daukar Horo

Home Ana Rikici Tsakanin Mourinho Da Paul Pogba A Filin Daukar Horo
Ku Tura A Social Media
Rahotanni daga kasar ingila sun bayyana cewa mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho da dan wasan kungiyar, Paul Pogba sunyi rikici a lokacin da kungiyar take daukar horo a filin daukar horon kungiyar bayan da Pogba yayi zargin cewa Mourinho yana kallonsa a matsayin wanda yasa kungiyar bata kokari.

Hakan yasamo asaline sakamakon halin da kungiyar ta shiga na rashin lashe wasanni a yan kwanakin nan bayan da kungiyar ta lashe wasanni biyu kacal cikin wasanni biyar da kungiyar ta buga.

Sau biyu Mourinho yana cire Pogba acikin wasannin da kungiyar ta buga sannan kuma sau uku yana ajiyeshi a benci wanda hakan yasa aka fara rade radin cewa akwai matsala a tsakanin mutanen guda biyu.

Wasu rahotannin sun bayyana cewa Mourinho yana zargin Pogba bias zakewa da yake wajen shiga aikin mai koyarwa abinda kuma Mourinho bayason.

Sannan an kuma bayyana cewa Mourinho yana gayawa dan wasan bakar Magana agaban ragowar yan wasan kungiyar wanda kuma Pogba yake ganin kamar yana wulakantashi.
Tuni aka fara rade radin cewa Pogba yafara tunanin barin kungiyar bayan daya bukaci wakilinsa daya fara neman kungiyar da zata siyeshi domin yana son barin kungiyar a karshen kaka mai zuwa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: