Sunday, 18 February 2018
Ɗan Jihar Katsina ya jawowa Najeriya abin alfahari a Duniya

Home Ɗan Jihar Katsina ya jawowa Najeriya abin alfahari a Duniya
Ku Tura A Social Media
Bashir Dodo yayi wani nazari da zai agazawa masu cutar idanu

- Dr. Bashir Dodo Malami ne Matashi ‘Dan asalin Jihar Katsina ne

- Wannan bincike da aka yi ya ci lambar yabo a wata Jami’ar waje

Mun samu labari cewa wani hazikin Matashi da ya fito daga Jihar Katsina yayi suna a Duniya inda ya kammala karatun sa na Digiri na uku watau PhD a wata Jami’ar kasar waje kwanan nan.


Binciken Dodo yayi zarra a wata Jami’ar Kasar waje

Bashir Isa Dodo wanda Malami ne a Jami’ar Katsina a fannin ilmin komfuta ya kirkiro wata hanya da za a bi ta taimakawa masu fama da larurar rashin lafiyan ido a Duniya. A Jami’ar ta Birnin Brussels wannan ta sa Dodo ya karbi lambar yabo.Wannan bincike na Bashir Dodo ta sa ya karbi kyauta a kasar inda aka tashi taron BIOMAGING na masana a shekarar bana babu kamar sa. Binciken na sa zai taimaka wajen gyara sashen retina da ke cikin idanun ‘Dan adam nan gaba a Duniya.

Likitocin idanu a Duniya za su amfana da wannan gudumuwa da Dr. Bashir Dodo ya kawo. Bashir asalin ‘Dan Jihar Katsina ne kuma yayi Digiri da Digirgir a fannin Komfuta inda ya kamalla a 2012.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: