Thursday, 8 February 2018
Ali Nuhun Da Adam A Zangon Duka Azzalumai Ne, Inji Ali Artwork

Home Ali Nuhun Da Adam A Zangon Duka Azzalumai Ne, Inji Ali Artwork
Ku Tura A Social Media

Sakamakon rikicin da ya so barkewa tsakanin Ali Nuhu da Adam A Zango hakan ne ya sa magoya bayan bangarorin biyu suke ta cece kuce akan haka.

Wannan dalilan ne ya sa Ali Artwork ya yi fashin baki akan wadannan jarumai a shafin sa na instagram.

Ga bayanin nasa kamar haka:-

Duk abunda kuka ga suna yi (Ali da Adamu) suna sane kuma su suke kirkirar hakan don su motsa jam’iyya kar a ce ai kwana biyu an manta da su. To ku sani ku Masoyansu ku suka mayar mahaukata. Idn baku manta ba a shekaru baya sun taba shirya irin wannan rikicin nasu mu ka zo muka yi ta cece kuce a kai. Amma daga karshe mai hakan ta haifar sai suka maida mu ba mu san komai ba. Dan haka kusan duk wanda ya sa kansa sai ya yi da na sani. 

Ni yanzu babu ruwana da kowa a cikinsu dan ba wanda a cikinsu zai iya kashe min matsalar dubu 200,000. Kowa a cikinsu na zauna da shi ba wanda bai more ni ba akan harka ta ta editing. Amma babu wanda na taba yi wa aiki ya dauki dubu dari 100,000 ya ba ni, idan kuma da akwai ya fito ya karyata ni.

Sai dai kai ta bautar banza. sun fi so kullum ka yi ta ba su girma suna zalintar ka to ku sani an yi walkiya mun ga kowa. Kyar Nake Kallonku.

Ba ruwa na da rigimar wani, ni ma ta kaina nake. Idan kana yi da ni, ina yi da kai, idan ba ka yi da ni, ni ma baruwa na da kai.

Ku kuma Ali da Adamu duk sanda kuka ga dama ku shirya, ku ta dama ni ko a jikina, ko kuma mutum ya bar industiri din tunda ba da ita aka haife shi ba, don haka mu za mu ciyar da harkar gaba insha Allah, tunda ku sai hassada da munafurci da gwara kan al'umma, ku je ku yi ta yi. Don haka ni na dogara da Allah shi ne gatana ba wani mutum ba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: