Sunday, 25 February 2018
Akan Naira Dudu Bari Biyu Basu Sanya Ayi Lalata Dani Inji Maryam Both

Home Akan Naira Dudu Bari Biyu Basu Sanya Ayi Lalata Dani Inji Maryam Both
Ku Tura A Social Media
Wani bawan Allah me suna Muhammad Usman ya turawa tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth sako inda yake rokonta cewa tazo suyi holewar hutun karshen mako tare a Abuja, yayi alkawarin cewa zai baka tsabar kudi naira dubu dari biyu idan ta yarda.

Saidai Maryam ta mayarwa da Muhammad martanin cewa dubu dari biyu ba komai bane a gurinta, ta kara da cewa idan ma yana son dubu dari biyu to ya aiko mata da lambar ajiyar bankinshi zata bashi domin shine matsiyaci, ita ba matsiyaciya bace.

Maryam dai ta kara da cewa tana kashe dubu dari biyun da yake tun kahon zai batane wajan sayan katin waya da alewa, dan ma kar yayi tunanin wai wata tsiyane a gurinta. Tace kai koda miliyan dari biyu yace zai bata ba zata yarda ba domin bata ganin girman mutane irinshi.

Maryam ta kara da cewa daga ji shi wannan Muhammad din sabon shigan wannan harkane, inda tace koda yake tarbiyya daga gida take farawa, babanshi ma haka yake shiyasa shima yayi gado, a karshe tace yaje ya nemi na kan titi domin jikinta da lokacin ta bana sayarwa bane, tana da aikinta, tana neman kudinta kuma tana alfahari da hakan.
A karshe ta kira Muhammad da matsiyaci inda tace watau shi gashi dan gidan masu kudin Duniya(zai nuna mata kudi), taso ace gaba da gaba ya gaya mata wannan magana da yasha mari.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: