Monday, 1 January 2018
'Yan Nigeria ba su da hakuri— Muhammadu Buhari

Home 'Yan Nigeria ba su da hakuri— Muhammadu Buhari
Ku Tura A Social Media

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce 'yan Najeriya ba su da hakuri na son rayuwar su ta inganta cikin gaggawa fiye da karfi da arzikin da kasar ke da shi.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi kan bukin sabuwar shekarar 2018.

Ya ce ya jima yana bibiyar al'amuran da ke gudana musamman muhawara da wasu ke yi na batun sake fasalin kasar, kuma idan aka hada ra'ayoyin al'umma wuri guda, ya yi amannar matsalolin kasar sun fi karkata ne kan hanyar da ake bi ba tsarin da ake kai ba.

Ya ce babu wata doka ko wani al'amari na dan Adam da ya cika dari bisa dari, a don haka duk wani tsari da aka bullo da shi wajibi ne a rika inganta shi lokaci zuwa lokaci domin ya da ce da ci gaba ta fuskar siyasa da tattalin arzikin kasa.

'' Ya ce mu 'yan Nigeria muna da gajen hakuri muna son rayuwar mu ta inganta cikin gaggawa fiye da karfi da arzikin da kasar ke da shi.

Shugaba Buhari ya ce idan aka hada ra'ayoyin al'umma wuri guda, ya yi amannar matsalolin mu sun fi karkata ne kan hanyar da ake bi ba tsarin da ake kai ba.
Shugaba Buhari ya bayyana takaicin sa kan matsalar karancin man fetur inda ya ce abu ne da ba za'a lamunta ba.

Ya kuma sanar da kokarin da gwamnatinsa ke yi na samar da ababen more rayuwa ga al'umma, kamar samar da hanyoyi da wutar lantarki da kuma gina layukan dogo na jirgin kasa.

Shugaban kasar ya ce kofar gwamnati a bude take wajen karbar shawarwari don ciyar da kasar gaba, inda ya bukaci 'yan siyasa su guji furta kalamai da za su janyo rarrabuwar kai yayin da aka fara gangamin siyasa a 2018.

Ya kara da cewa gwamanti zata ci gaba da fafutikar ganin ta kare rayukar al'ummar kasar kuma za'a dauki matakai sosai wajen ganin an shawo kan matsalar masu satar mutane don neman kudin fansa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: