Saturday, 13 January 2018
Watar Sabuwar : Babban Burina Shine In Auri Shugaban Kasa Muhammed Buhari - Jarumar Hausa Film Fati Shu'uma

Home Watar Sabuwar : Babban Burina Shine In Auri Shugaban Kasa Muhammed Buhari - Jarumar Hausa Film Fati Shu'uma
Ku Tura A Social Media

" Wallahi Tallahi a rayuwata ban taba samun Da Namijin daya shiga raina nake masifar sonshi sannan nake burin auren shi, kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, sannan bani da burin da ya wuce in kasance Amaryar shi".

Kalaman matashiyar jarumar Hausa Film  Fati Abubakar kenan, wacce aka fi sani da Fati Shu'uma a yayin wata tattaunawa da jaridar Blue Print tayi da ita makon da ya gabata a birnin Kano.

Fati Shu'uma ta cigaba da cewar duk inda ake neman namiji kyakkyawa to Buhari ya kai, gashi fari dogo mai wushirya sannan ga jarumtaka, wallahi duk Macen da ta auri Buhari ta dace, kuma hakika na kamu da sonshi fiye da duk wani Da namiji a fadin duniyar nan, Allah kasa in auri Buhari inji Jarumar.

Hakika na sani uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari kyakkyawar mace ce, amma duk da haka ina fatar gogaiya da ita wajen mijinta, sannan ina rokon 'Yan Nijeriya su sanya ni a 

cikin addu'a Allah ya cika mini wannan burin nawa, sannan wanda keda halin sanar da shugaban kasa wannan burin nawa don Allah ya taimaka mini.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: