Tuesday, 9 January 2018
Ta Faru Ta Kare : Hukumar Moppan Ta Yafe Wa Jaruma Rahama Sadau

Home Ta Faru Ta Kare : Hukumar Moppan Ta Yafe Wa Jaruma Rahama Sadau
Ku Tura A Social Media


Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce ta
yafe wa fitacciyar jarumar finafinan Hausa Rahama Sadau dukkan laifukan da ta yi, wadanda suka janyo aka hana ta yin fim.

Shugaban hukumar, Isma'ila Na'abba Afakalla, ya shaida cewa, "A shirye muke mu soma tace fina-finan da za ta rika fitowa a ciki da kuma wadanda take daukar nauyinsu".

Afakalla ya kara da cewa sun dauki wannan
mataki ne bisa la'akari da gafarar da jarumar ta nemi a yi mata kwanakin baya.

A cewarsa, "Wannan baiwar Allah ta zo ofishina a shekarar da ta wuce inda ta nemi gafara kan
abubuwan da ta yi a baya; na gaya mata ta je ta nemi gafarar Gwamna da Sarkin Kano kuma ta fito a gidan rediyo ta nemi afuwarsu da ta
al'umar da take ciki.

"Don haka a matsayinmu na 'yan-Adam wadanda
kullum muke cikin kuskure, so muke a ja mutum a jiki kada ya fandare, shi ya sa muka yafe mata. Duk lokacin da mutum ya yi laifi ba a rufe masa hanyar tuba. Kuma ko yanzu ta kawo fim za mu tace shi", in ji shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: