Tuesday, 30 January 2018
Sharhin fina finai Abubuwan Burgewa Da Kura Kurai Da A cikin Fim Din Hasashe

Home Sharhin fina finai Abubuwan Burgewa Da Kura Kurai Da A cikin Fim Din Hasashe
Ku Tura A Social Media
Suna: Hasashe
Tsara labari: Abdullahi Amdaz, Bashir Dan Rimi.
Furodusa: Nazir Auwal Dan Hajiya
Director: Ali Gumzak
Kamfani: Ali Nuhu Team
Jarumai: Ali Nuhu, Garzali Miko, Hafsat Idris Barauniya, Sadiya Adam, Bilkisu Abdullahi, Ammar Umar, Hajara Usman da Amina Maiduguri.

Abubuwan birgewa:

1-wakokin fim din sun yi dadi sun kayatar da masu kallo
2- Jaruman sun yi kokari wurin fito da labarin yanda mai kallo zai fahimta.

Kurakurai:

1- Shin wanene Najib? mai kallo kawai ya gan shi yana yaudarar ‘yan mata kuma daga bisa ni ya yi aure ko iyayensa ba’a taba nunowa ba ko anyi maganarsu ba.
2- Shin duk ‘yan matan da ya ke kulawa basu da gidan iyaye sai dai kullum a gansu a wurin shakatawa? sannan ya aka yi idan Najib yazo gurin shakatawa ‘yan matansa kullum ake arashi suke haduwa ko kuma sanar musu yake yi shi da ya ke abinsa a boye baya san asirinsa ya tonu?

3- Menene asalin sunan jarumin labarin acikin fim din (Garzali miko) masu kallo sunji wasu suna kiransa da Najib wasu kuma Kabir wasu kuma Abdurrashid har fim din ya kare ba’a tabbatar da tar tibin guda daya ba.

4- Akwai wurin da Najib yake chatting da burwarsa a gidansa kawai aka ga ya ajiye wayar ya ta shi matarsa kuma aka ganta ta zo ta dauka tana dubawa a wurin an nuna kamar don ta dauka ya ajiye ya ta, duk boye mata sirrikansa da yake.

5- An nuna Jawahir tana da karamin ciki a hotan gaba wanda aka kuma nuno su sai aka ga har ta haihu da aka kuma nuno su sai kuma aka ga har ‘yar ta girma dab da dab din ya yi yawa duk da fim ne ya kamata ace idan ma za’ayi haka to ace an rubuta bayan lokacin kaza.. sannan aga wani abin kuma ya faruwa.

6- Zaren labarin bai tafi ya dire ba sai ya dinga tafiyar hawainiya idan aka kunno matsala mai kallo ya karkatu akan ya ga ya abin zai karke sai kuma a sake kunna wata ba tare da an warware waccen ba har fim din ya kare abubuwa da yawa ba’a ga karshensu ba.

7- Camerar daukar hoto bata fita yadda ya kamata ba a fim din.
8- Bai kamata a ga mai aikin gidan mujahid ta ce masa wai bari ta shiga wanka ba shi kuma yace tohh a gaske hakan zai yi matukar wahalar faruwa menene alakarsu? tun da ba matarsa bace ina ruwansa da wankan ta.

9-Menene aikin da Najib ya fadawa budurwarsa zata yi masa a gidan Mujahid? tunda mai kallo bai ga wani abu da ta yi ba a zuwanta gidan na bincike ba kamar yanda Najib ya nuna.

10- A gaske zai yi matukar wahala budurwa ta yi wa saurayinta korafin yana kula kulan ‘yan mata sannan ya ce mata wai shi ba aurensu zai yi ba karya kawai yake yi musu kuma budurwar bata nuna wani bacin ranta ba, kawai ta yadda da abinda ya fadamata duk da an saka musu rana kamar yanda Najib ya fadawa Fadila.

Karkarewa:

Labari ne mai kyau amma bai sami tsari mai kyau ba shiyasa ya ruguje kuma an gaza wurin fito da ma’anar labarin sannan an gaza bai wa labarin karshe yanda ma mai kallo zai fahimci makasudin labarin. Allahu a’a lamu.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: