Tuesday, 16 January 2018
Rikicin makiyaya Shugaba Buhari ya gana da gwamnan jihar Benuwe da sarakunan gargajiya na jihar

Home Rikicin makiyaya Shugaba Buhari ya gana da gwamnan jihar Benuwe da sarakunan gargajiya na jihar
Ku Tura A Social Media
Shugaban yace jami'an tsaro zasu cigaba ga tabbatar da tsaro ga al'ummar jihar kana zasu iya bakin kokarin su wajen hukunta duk wanda ke da hannu kan kashe-kashe da ya faru

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya gane da manyan masu ruwa da tsaki na jihar Benuwe kan rikicin makiyaya.
An gudanar da zaman ne a fadar shugaban dake Villa yau 15 ga wata da misalin karfe 3 na rana.

Bayan tattaunawar da suka yi, shugaban yace sakon da ya sanar masu shine zai cigaba da tsayawa kan bakan alkawarin da ya dauka ma yan Nijeriya na tabbatar da tsaron rayukan su.
Shugaban yace jami'an yan sanda da yan hukumar DSS da sojoji na bakin kokarin su wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar Benue kana zasu cigaba da aikin su har sai an hukunta wadanda suka aikata kashe-kashen da ya faru a jihar.

Gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom ya jagoranci tawagar sarakunan gargajiya da manyan masu ruwa da tsaki a harkar siyasa na jihar zuwa wajen taron.
Hakazalika ministan tsaro da ministan ayyukan cikin gida tare da mai baiwa kasa shawara kan harkar tsaro da shugaban hukumar DSS sun halarci taron.
Shugaban ya gudanar da taron ne domin samun mafita kan kisan da makiyaya suka gudanar a jihar Benuwe.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: