Sunday, 21 January 2018
Rabi'u Rikadawa ya bayyana cewa hakika yafiyar da aka yi wa jarumar Rahama Sadau abu ne mai kyau

Home Rabi'u Rikadawa ya bayyana cewa hakika yafiyar da aka yi wa jarumar Rahama Sadau abu ne mai kyau
Ku Tura A Social Media
Fitaccen jarumin nan a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Rabi'u Rikadawa ko kuma 'Dila' kamar yadda ake kiran sa a tsakanin abokan sana'ar sa ya bayyana cewa ya ji dadi da gwamnan Kano ya yafewa jaruma Rahma Sadau.


kuma wannan ya nuna cewa gwamnan jihar Dakta Abdullahi Umar Ganduje cikakken shugaba ne mai sauraren talakawan sa.


NAIJ.com dai haka zalika ta samu cewa jarumin ya kuma bayyana cewa daman dai duk dan adam ajizi ne kuma ya kamata idan mutun yayi laifi sannan kuma ya roki yafiya to a yafe masa domin samun maslaha.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar masu shirya fina-finai watau MOPPAN tayi fatali da batun yafiyar da akayi wa jarumar inda ta kuma ce ita sai kotu zata raba su.

Tun farko dai a shekarar da ta gabata ne aka dakatar da jarumar daga dukkanin fina-finan Hausa saboda ta rungumi wani mawaki yayin da suke daukar wata wakar sa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: