Wednesday, 24 January 2018
Obasanjo Tsohon shugaban kasa ya caccaki gwamnatin Buhari, yayi kira na ya dakatar da maganar zarcewa

Home Obasanjo Tsohon shugaban kasa ya caccaki gwamnatin Buhari, yayi kira na ya dakatar da maganar zarcewa
Ku Tura A Social Media
Yace shugaban yayi aiki ne kasa da yadda jama'a suka yi tsammani bisa ga haka ya dakatar da anniyar sa na zarcewa a zaben 2019

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya caccaki gwamnatin shugaba muhammadu Buhari bisa ga rashin aiwatar da kyawawan ayyuka kana ya shawarce shi da kada ya nemi zarcewa a zaben 2019.

Tsohon shugaban kasa ya bayyana ra'ayin sa game gwamnatin shugaba Buhari a wata faifan takarda wanda aka fitar ranar talata 23 ga wata janairu 2018.
Cikin takardar mai taken "The Wat Out: A Clarion Call for Coalition for Nigeria Movement", Obasanjo ya bayyana wurare da gwamnatin Buhari ta gagara samun nasara musamman a bangaren kasuwanci.

Yace shugaban yayi aiki ne kasa da yadda jama'a suka yi tsammani bisa ga haka ya dakatar da anniyar sa na zarcewa a zaben 2019.

Tsohon shugaban kasa wanda yayi mulki tsakani 1999 zuwa 2007 yayi kira ga shugaba Buhari da ya zamanto mai bayar da taimako a shugabancin kasar nan gaba domin yin haka zai fi muhimmanci a kasar dama sauran kasashen duniya.

Bugu da kari Obasanjo ya soki shugaban bisa ga akidar nuna fifiko a gwamnatin sa tare da irin dabi'ar rikon-sakai- na ksashi na shugaban ke nuna ga muhimman abubuwa dake wakana a kasar.

Daga karshe Obasanjo yace shugaba Buhari baya da kwakwarar ilimin siyasar kasar kuma bisa ga wannan dalilin ya haifar da rarrabuwar kai a fadin kasar.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: