Wednesday, 17 January 2018
Nayi Alkawalin Sai Na Aure Malamin Islamiya Inji Fati Muhammad

Home Nayi Alkawalin Sai Na Aure Malamin Islamiya Inji Fati Muhammad
Ku Tura A Social Media
Sanannar jarumar nan a da ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood a shekarun baya watau Fati Muhammad ta bayyana aniyar ta na auren wani fitaccen malamin addinin Islama mai suna Mallam Datti Assalafi.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata budaddiyar wasika da ta rubutwa malamin a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook a jiya Talata, 16 ga watan Janairu biyo bayan abun da ta kira cin mutuncin da yayi mata da kage da sharri.


NAIJ.com dai ta samu cewa jarumar ta yi wa malamin budaddiyar wasika ne biyo bayan wani rubutu da yayi akan ta inda ya zarge ta da biyewa masu kudi da 'yan siyasa suna kwana da su domin samun kudi.

Sai dai jarumar ta bayyana hakan da yayi a matsayin abun takaici inda tace in ma har gyara ko nasiha yake so yayi mata to ba ta hanyar cin ya kamata yayi mata ba don ba zai yi wa kanwar sa ko diyar sa hakan ba.

Daga karshe sai jarumar ta bukaci malamin da ya fito ita kuma a shirye take da ta aure shi idan dai har da gaske yake yi so yake yi tayi aure.


Share this


Author: verified_user

0 Comments: