Friday, 5 January 2018
Na yi kura-kurai da yawa saboda daukakata — Adam Zango

Home Na yi kura-kurai da yawa saboda daukakata — Adam Zango
Ku Tura A Social Media


Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adam A. Zango ya ce ya yi kura-kurai da yawa a rayuwarsa.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook da Instagram, Zango ya ce amma lokaci bai kure masa na gyara su ba.

A cewarsa, "Na yi kura-kurai da yawa a sanadiyyar daukaka...sai dai lokaci bai kure min ba!! Gyara ya zama dole...Allah ya ba mu sa'a".
Dan wasan na Kannywood bai yi cikakken bayani kan abin da yake nufi ba, sai dai a wata hira da BBC a kwanakin baya, ya ce ya yi nadamar fitowa a fina-finai da dama.
Jarumin ya ce wani abu da yake ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda wasu 'yan boko suke masa kallon jahili duk kuwa da cewa "na yi karatun bokon sannan kuma ina da ilimin addini."
Batun ilimin boko ne dai ya taba sa Adam ya wallafa wani habaici a shafinsa na Instagram da bai yi wa wasu 'yan boko dadi ba, al'amarin da har ya sanya jarumin yin da-na-sani.

Fitaccen jarumin ya ce a kullum yana kwana yana tashi da bakin cikin zargin da wasu suke yi masa na zama dan luwadi (neman maza).
Wannan ne ya sa a wani lokaci a baya jarumin ya dauki Alkur'ani ya rantse cewa bai taba neman wani namiji da lalata ba.
"Wannan abin yana hana ni barci, kai har ma na taba zuwa neman aure amma aka hana ni saboda haka," in ji Zango.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: