Friday, 19 January 2018
Mai Tsoron Aradu : Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso

Home Mai Tsoron Aradu : Zan ziyarci Kano duk da adawa - Kwankwaso
Ku Tura A Social Media
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso ya karyata rahotannin kafofin watsa labarai na cewa ya soke shirinsa na ziyartan jiharsa a ranar 30 ga watan Janairu saboda rashin lafiya.

Ziyarar nasa ya haifar da tashin hankalin siyasa a jihar inda wasu yan siyasa ke ikirarin cewa Sanata Kwankwaso zai ziyarci jihar ne saboda ya tsokano yan adawansa da kuma gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

Kwanakin baya ne yan sanda suka gayyaci wani kwamishinan jihar, da ya bukaci magoya bayansu da su jefi sanatan a duk lokacin da ya ziyarci jihar.


Da yake magana ta bakin mai bashi shawara a kafofin wata labarai, Binta Rabiu, dan majalisan ya ce zai ziyarci Kano kamar yadda aka tsara.

Kwankwaso ya bayyana rade-radin rashin lafiyarsa a matsayin aikin “gwamna Ganduje da yan fadarsa.”

Share this


Author: verified_user

0 Comments: