Kannywood

Kunji wata sabuwa : Mu Matan Fim Mafi Yawan Mu Maza Auren Sha’awa Suke Yi Damu Shi yyasa Auren Mu Baya Kai Wa ko Ina- Inji Fati Muhammad

 

 

Namiji ne zai zo miki da maganar Aure kuma zai yadda ya kashe ko nawa ne don ya mallake ki a matsayin matar shi, daga baya idan ya sami biyan bukatar sha’awar sa sai ya sake ki.

 

Jaruma kuma kwararra a fagen masana’antar shirya fina-finan Hausa Fati Muhammad ita ta bayyana haka a wata hira da aka yi da ita game sa rikita rikitar mutuwar Auren Matan Fim.Fati Muhammad tace babu macen da zata yi Aure sunnar Annabi kuma tayi farin cikin mutuwar Auren, Mazan ne ke yi musu Auren sha’awa.

 

Amma abun haushi mutane laifin su suke gani sai suce wai sune basu son zaman Aure; kuma masu yi musu wannan kallon suma zaka iya zuwa gidajen su ka tarar da Zawarawa kusan guda uku ko hudu, to muma matan Fim ba daga sama muka fado ba haifar mu aka yi; inji Fati

 

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button