Friday, 19 January 2018
Jarumar fina-finai, Liz Anjorin ta bayyana dalilin musuluntar ta

Home Jarumar fina-finai, Liz Anjorin ta bayyana dalilin musuluntar ta
Ku Tura A Social Media
DAGA HAUSA TIMES
Fitacciyar jarumar fina-finan kudanci, Nollywood, Liz Anjorin wacce ta musulunta ake ce mata Aisha ta yi bayanin abunda ya jawo ta karbi musulunci.

Yar wasan fim din wacce asalinta Kirista ce haka ma iyayenta kwatsam anjiyo ta musulunta a inda hakan ya janyo cece-kuce.
To sai dai jarumar fina-finan ta fito karara inda ta bayyana dalilin da tunzurata ta bar addinin kiristanci ta musulunta.

A shafinta na Instagram ta rubuta cewa “A lokacinda mahaifiyata ta rasu duk cocina suka ki karban ta, munje fiye da coci 10 amma suka ki karbar gawar ta domin suyi mata sutura a bizne ta.”
Liz kafin ta musuluntaTa ce duk da cikin halin rashi da ta tsinci kanta a wancen lokacin amma haka muja’mi’un sukayi watsi da ita duk da cewa sun san a lokacin tana cikin tsananin bukatar a taimake ta.

Tace sai addinin da ba nawa ba (musulmai) su suka taimake ni suka yiwa uwa ta sutura, “Bayan sun gama dakyar wani coci ya bayar da wurin da aka bizne ta a makabartar cocin.”
Hausa Times ta ruwaito jarumar na cewa tun daga lokacin ta kudurce a ranta zata tafi Hajji ta musulunta. Kuma hakan akayi tun daga lokacin taji sha’awar musulunci ta shiga har yau kuma tana cikinsa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: