Sunday, 21 January 2018
Hotunan kyakykyawar amarya da ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta

Home Hotunan kyakykyawar amarya da ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta
Ku Tura A Social Media
- Amarya ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta

- Ta yayyaga kayan amarcinta

- Ana zargin kishiyar uwarta da yi mata asiri

A ranar da ya kamata ta kasance mata ranar farinciki da alfahari, sai ga shi wata kyakykyawar amarya ta haukace ana tsaka da shagalin bikinta.


Amarya yayin da ta Haukace ana tsaka da shagalin bikinta
Wani shaidar gani da ido ya ce amaryar ta fara haukan ne yayin da suke tsaka da taka rawa ita da angonta. Ya ce amaryar ta fara da cire gyauton da take sanye da shi kafin daga bisani ta fara yayyage kayan dake jikinta.


Duk da ya zuwa yanzu ba'a tantance da mene ne ya haddasa haukacewar amaryar ba, 'yan uwanta sun dora laifin abinda ya samu amaryar a kan kishiyar uwarta, wacce suka ce bata son ganin amaryar ta yi aure.

Wannan abin tausayi ya faru ne a garin Masaka dake kasar Uganda.

Saidai rahoton da muka samu bai ambaci sunan amaryar ko angonta ba, saidai jama,a a dandalin sada zumunta sun cigaba da tofa albarkacin bakinsu a kan faruwar al,amarin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: