Saturday, 6 January 2018
Fitacciyar mawakiya Ummu Ahmad Baba wanda aka fi sani da Ummi Nagarta ta caccaki manyan mawakan Kannywood

Home Fitacciyar mawakiya Ummu Ahmad Baba wanda aka fi sani da Ummi Nagarta ta caccaki manyan mawakan Kannywood
Ku Tura A Social Media
Fitacciyar mawakiya Ummu Ahmad Baba wanda aka fi sani da Ummi Nagarta ta caccaki manyan mawakan Kannywood da kuma ’yan kasuwa bisa zargin yadda suke yi wa matasan mawaka da masu tasowa rikon-sakainar-kashi.

Mawakiyar wadda ta yi fitattun wakoki irin su ‘Uwar Adashi’ da ‘Wuta Sallau’ da ‘Babuje’ ta bayyana hakan ne a lokacin da take tattaunawa da Aminiya a ranar Litinin da ta gabata.

Mawakiyar ta yi korafin cewa kimanin shekara biyar ke nan da ta yi wakokin albam din ta guda uku, amma ’yan kasuwa sun ki saye, dalili kuwa shi ne manyan mawaka sun bata su, ba su nuna cewar idan sabon mawaki ya yi albam su saya ba.
Ta ce, “’Yan kasuwa sun fi ganin darajar mawakin da tauraransa yake haskakawa. Ba sa duba ma’anar albam. Sai ka ji suna cewa gaskiya idan na saya asara zan yi.
Ta kara da cewa: “Har shekara uku da ta wuce na nemi wani dan kasuwa, ba sai na fadi sunansa ba, na ce masa zan buga da kudina in ya so sai ya raba wa ’yan kasuwa, daga baya ya nuna mini kawai in ba shi ya buga, amma ba biya na zai yi ba.”
Ta ce alhalin da bazar mawaka ’yan kasuwa suke taka rawa, tun da da fasahar mawaka suke ciyar da iyalinsu, amma kuma mawaka ne abubuwan wulakantawa.
Ta ce, “Mu ne ya kamata ’yan kasuwa su nema domin sayan albam din mu, amma mu ne muke bin su don su saya saboda harkar ta lalace sai gyaran Allah. Haka za ka ga ’yan kasuwa suna hawa manyan motoci, sun kuma gina gida mai tsada, amma mawaki yana yawo a kasa, kuma da damar mawaki ya samu gida da mota tun da basirarmu muka sayar masa yake ciyar da iyalinsa.”

Ta ce, mawaki mutum ne wanda Allah Ya ba shi baiwar isar da sako ta hanyar waka, amma mawaki ba shi da wata kima a idon ’yan kasuwa. “Da haka ’yan kudu suka fi mu, saboda ’yan kasuwarsu suna daraja mawakansu na R&B. Amma kullum mu ne a baya.”

Ta yi zargin cewa ’yan kasuwa sun hada kai, bakinsu daya amma mawaka kansu ya rabu, domin ba ta ga wani ci gaba da suka samu ba, kullum jiya ya yau, domin suna da basira ’yan kasuwa suna wulakanta su.
Ta ce, “Ya kamata a kafa mana kwamitin da za su rika sanya ’yan kasuwa su sayan albam din da muka yi, kuma mawaka su amshi ragamar buga albam a hannun ’yan kasuwa tun da dama tun farko haka ya dace a ce an yi, mawakanmu suka yi sakaci ’yan kasuwa suke wulakantamu.”

Ta ce, alumma kullum suna so su ji sabuwar waka daga wurin sabbin mawaka amma ana dakile su.

Ta yi zargin cewa su ma manyan mawaka suna da nasu laifin, “Akwai matasan mawaka sama da dubu uku a Kano, amma wasu kawai ake ji a matsayin mawaka, kimanin mutane 10 zuwa 20, mu an mayar da mu ’yan cikon kujera sai a hada taron mawaka a nemi kudi, amma ba za ka ji an taimaka wa mawaka don su ci gaba ba.
“A Shekarun baya aka samu muka sayin fom da sunan za a kawo mana gyara, amma shiru kake ji. Da an yi magana sai a ce ai mu ba mawaka ba ne, bayan ana shiga rigarmu mu ana famtamawa.” Inji ta.

Ta ce, sai a hada taro a kira manyan kasa su zo su ga mawaka amma, daga nan manyan su ci gaba walwala, sauran mawaka masu tasowa an mayar da su ko oho.
“Idan ba a kawo gyara ba, to haka za mu yi ta zama ana raina mu, bayan mu ba jahilai ba ne. A yanzu kusan kullum sai masoya sun bugo waya suna tambayar yaushe albam dina zai fita, na gaji da ba su hakuri, shi ya sa na yi magana don su gane inda gizo ke sakar.”

Ta ce, idan har da da tsayayyiyar kungiyar mawaka, to da mawakan ne ya kamata su ja wa ’yan kasuwa aji.
Ta kuma kara zargin cewa duk tallafin da gwamnati take bayarwa, to manyan mawaka ne suke sama da fadi da shi.

Ta ce, “’Yan kudu sun fi mu hadin kai, wani ma ihu zai yi a wakarsa, amma haka za a saya, ya samu riba, haka ake damawa da su saboda suna da hadin kai. Amma a Arewa sai mawaki ya yi wa dan kasuwa karamar murya, sannan zai sayi albam dinsa, bayan mu ne jigonsu, idan ba mu yi waka ba ta yaya za su ciyar da iyalansu.”
A karshe ta bukaci gwamnati ta kafa kwamitin da zai rika lura da mawaka, saboda ta hanyar waka ake tallar ’yan siyasa har ake zabarsu, kuma ake fada wa duniya aikin da suka yi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: