Wednesday, 10 January 2018
Duniya Ina Zaki Da mu : An Cafke Amaryar Da Ta Kashe Mijinta A Jihar Kano

Home Duniya Ina Zaki Da mu : An Cafke Amaryar Da Ta Kashe Mijinta A Jihar Kano
Ku Tura A Social Media

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi nasarar cafke wata Amarya da ake zargi ta kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba cikin abinci.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Magaji Majiya ya shaida wa manema labarai cewa 'yan uwan mijinta ne suka kai rahoto ofishin 'yan sanda da ke Kofar Wambai a birnin Kano.

Ya ce ana zargin Amaryar da sanyawa mijinta guba ne ranar alhamis 4 ga watan Janairun 2018 kuma ya rasu ne bayan kwana guda da sanya masa gubar.

Kakakin rundunar ya ce a lokaci da 'yan sanda suka isa gidan sun tarar cewa Amaryar ta tsere kafin daga bisani aka cafke ta ranar Litinin din da ta gabata.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun ce an yi wa Amaryar auren dole ne.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: