Sunday, 7 January 2018
Dandalin Kannywood: Gwarazan Matasan Jarumai Maza A 2017

Home Dandalin Kannywood: Gwarazan Matasan Jarumai Maza A 2017
Ku Tura A Social Media

Umar M.shareef: Mawakin da ya shiga farfajiyan fim da kafar dama tun bayan fitowarsa a “Mansoor” masu shirya fina-finai na Kannywood sun kara bashi damar fitowa fina-finai daban daban. Umar M. Shareef ya tara dinbin masoya ba ma a kasar nan ba har ma kasashen ketare, musamman a kafafen sa da zumunta. Wokokin sa na kan gaba gurin cin kasuwa a shekarar 2017, daga cikin wakokinsa da suka  yi fice a 2017 akwai”Hasashe”. A cikin sabouwar shekaran nan zai sake sakon wani sabon Fim mai suna “Mariya” tare da abokiyar aikinsa ta Fim din Mansoor Maryam Yahaya

Garzali Miko: Yana daya daga cikin jaruman da tauraruwarsu ta fara haskawa a shekarar 2017 kuma suka samu karbuwa sosai a Farfajiyar Kannywood, a cikin kwanakin nan ya yi fina-finai da dama, kuma ya taka rawar gani sosai musamman yadda ya nuna fasaharsa a fannin rawa. Harma ya fidda bidiyon wakokinsa da suka yi suna wanda daga ciki akwai (Hasashe.) Ado Gwanja: Adamu Isah wanda ake masa lakabi da Ado Gwanja yana daya daga cikin jaruman da tauraruwar su ta haska a shekarar 2017, musamman a wajen mata, don yana da kware wa matuka a duk harkokinsa guda biyu musamman a fannin wakokin biki, daga cikin manyan fina-finai da ya fito akwai Mijin Yariya, da Dan Kuka a Birni, da dai sauransu.

Abdul M. Shareef: Tun fitowarsa a cikin shirin Fin din “Jinin Jikina” wanda kungiyar Shareef Studio ta dau nauyi, Tauraruwarsa ke haskawa har yanzu, a shekarar 2017 ma yayi fina-finai da dama wasu sun fito wasu suna kan hanya. Daya daga cikin fina-finan sa da suka yi suna a wannan shekarar akwai “Jani Muje”. Shamsuddeen Dan Iya: Babu shakka wannan matashin jarumi ya shirya bayyanar da basirarsa na yin Fim, kuma ga dukkan alamu daraktoci sun gani a jikinsa, domin kuwa tun bayyanarsa a Fim din “Gamunan Dai” wanda kungiyar FKD Production suka dau nauyi, Daractoci ke rububinsa. Daga cikin Fina-finan da ya yi a 2017 kuma suka.

Ramadan Booth : Babu shakka wannan matashin jarumi shi ma ba baya bane wajen nuna bajinta da basirarsa na yin Fim, kuma da alamu shi ma daraktoci sun gani a jikinsa, domin kuwa tun bayyanarsa a Fim din “Gamunan Dai” wanda kungiyar FKD Production suka dau nauyi, Daractoci ke rububinsa, daga cikin fina-finansa da suka yi suna a wannan shekarar akwai “Talaka Bawan Allah”  wanda suka yi tare da Sarkin jaruman Kannywood Ali Nuhu..

Nuhu Abdullahi: yana daya daga cikin matasan jaruman da suka yi tashe a shekaran 2017, Nuhu Abdullahi haifaffen jahar legas a can yayi karatun firamari da sankanderi ya na da kwalin diploma a karatun Hausa da Turanci, baya kammala kuma sai ya gar zayo kano dan fara wasan hausa fim, ya fara samun karbuwa tin sanda sukayi fim din Gamu nan dai, daga nan ne kuma ya ci gaba da bayyana a manya fina-finan daya daga cikin fin din da yayi wannan shekaran akwai THIS IS THE WAY.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: